Ba zan sake takara ba – Shugaba Buhari

Ba zan sake takara ba – Shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace zaben da aka yi a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu, shine takara na biyar da yayi kuma shine na karshe, saboda haka yana so ya bar abun koyi a bayansa.

Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin zababbun Gwamnoni da Sanatocin jam’iyyar APC, a wajen liyafar cin abincin dare a ranar Litinin, 25 ga watan Maris a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Sai dai Shugaban kasar bai sanar da abunda yake so ya bari ba a ayan nashi, ya sanar way an majalisun cewa a wani abunda zai iya gudanarwa ba tare da samun goyon bayansu ba.

Ba zan sake takara ba – Shugaba Buhari
Ba zan sake takara ba – Shugaba Buhari
Asali: Twitter

“Wannan ne ya sa nake neman goyon bayan ku. Abin da ya faru a majalisar da ta gabata abin takaici ne, domin har yanzun ni ina ganin bai kamata a shige watanni bakwai ba, ba tare da an iya zartar da kasafin kudi ba. akwai aiki mai tarin yawa a gabanku."

Shugaban kasar ya yi alkawarin yin aiki tare da sabuwar majalisar ta 9, wajen samar da zaman lafiya, da bunkasar arzikin kasa, shugaban ya kuma yi godiya ga gwamnoni da sabbin Sanatocin a kan goyon bayan na su da fahimtar da suka nuna.

KU KARANTA KUMA: Kai tsaye: Yadda zaben gwamna ke gudana a jihar Adamawa

Shugaban Jam’iyyar ta APC Adams Oshiomhole, wanda ya yi magana da manema labarai na fadar gwamnati bayan liyafar cin abincin daren, yace, makasudin shirya taron shi ne domin karfafa hadin kai a tsakanin sabbi da kuma tsaffin ‘yan majalisyn dattawan, domin kafa sabuwar dangantaka a tsakanin sashen gwamnati da na majalisar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel