Wutar rikicin shugabancin majalisar dattawa a APC na kara ruruwa

Wutar rikicin shugabancin majalisar dattawa a APC na kara ruruwa

Wata kungiyar zababbun sanatoci da ke yiwa Shugaban masu rinjaye a majalisa, Ahmed Lawan kamfen a ranar, Laraba, 27 ga watan Maris tayi watsi da ikirarin tsohon Shugaban masu rinjaye a majalisa, Mohammed Ali Ndume a matsayin ba gaskiya ba.

Hakan ya rura wutar rikici a cikin jam’iyyar ta APC kan zabar shuaban majalisar dattawa na tara.

Aliyu Sabi Abdullahi, kakakin kungiyar sanatoci magoya bayan Ahmed Lawan, ya fada ma manema labarai a Abuja cewa ana sanar da zababbun sanatocin APC komai kan batun tsayar da Lawan a matsayin wanda ake son ya haye matsayin.

Wutar rikicin shugabancin majalisar dattawa a APC na kara ruruwa
Wutar rikicin shugabancin majalisar dattawa a APC na kara ruruwa
Asali: Depositphotos

Hakan ya kasance sabanin matsayar Sanata Mohammed Ali Ndume, wanda yayi kirari a ranar Talata, 26 ga watan Maris, cewa sanarwar da Shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole yayi na cewa an tsayar da Lawan ya zo ma zababbun sanatocin jam’iyyar a bazata a wajen taron cin abinci tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA KUMA: Dan marigayi Audu ya kaddamar da kudirinsa na takarar gwamna, ya sha alwashin kawo karshen yunwa

Ndume, a wani taron manema labarai a gidansa da ke Abuja a ranar Talata, yayi zargin cewa zabar Lawan da Oshiomhole yayi ba a tuntube su ba.

Koda dai Abdullahi bai ambaci sunan Ndume ba, ya bayyana cewa: “Babu kyau mutun ya dunga tsara karairayi.” yace a lokacin da Oshiomhole ya sanar da tsayar da Lawan, Shugaban jam’iyyar yayi Magana ne a gaban wasu gwamnonin jiha da suka hada da na Oyo, Kebbi da Borno.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel