Barayi sun kaiwa wani dan jarida hari sun yi awun gaba da matarshi, da matar wani dan majalisa

Barayi sun kaiwa wani dan jarida hari sun yi awun gaba da matarshi, da matar wani dan majalisa

- Matsalar tsaro na kara tsamari a Najeriya

- A jiya ne wasu 'yan bindiga su ka sace matayen wani dan jarida, tare da matar wani tsohon dan majalisa a jihar Nasarawa

A jiya Laraba ne 27 ga watan Maris, wasu 'yan bindiga su ka kaiwa wani babban dan jarida mai suna Suleiman Abubakar hari a jihar Nasarawa, inda suka yi awun gaba da matarshi mai suna Yahanasu Abubakar.

Barayi sun kaiwa wani dan jarida hari sun yi awun gaba da matarshi, da kuma matar wani dan majalisa
Barayi sun kaiwa wani dan jarida hari sun yi awun gaba da matarshi, da kuma matar wani dan majalisa
Asali: Twitter

Suleiman ya bayyanawa manema labarai cewar abin ya faru ne da misalin karfe 7 na dare, akan hanyar Gudi-Garaku da ke karamar hukumar Akwanga, cikin jihar ta Nasarawa.

KU KARANTA: Akwai yiwuwar a sake sabon zaben shugaban kasa a Najeriya

Suleiman ya kara da cewa 'yan bindigar sun cimma su ne a hanya, suka fara harbin motarsu, a lokacin da suke kan hanyar su ta zuwa wurin da matarshi zata yi bautar kasa. Ya ce harbin na su ne ya tilasta suka tsaya, inda suka yi awun gaba da matarshi da kuma matar wani tsohon dan majalisa, wacce suka rage mata hanya, sannan suka dauki wasu mata guda biyu daga wasu motocin da suka tare.

Sai dai shi kuma jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar ya ce, a yanzu haka hukumar ta tura jami'anta domin ceto matan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel