Mutane sun ki fita wurin zabe a jihar Adamawa

Mutane sun ki fita wurin zabe a jihar Adamawa

Da akwai alamun al'ummar Najeriya sun fara karaya da yanayin siyasar kasarnan, domin kuwa yau ne ake gabatar da zaben jihar Adamawa karo na biyu, amma mutane kowa ya fita harkarshi, babu wanda ya damu da zuwa wurin zabe

A yayinda ake gabatar da zaben gwamna karo na biyu a jihar Adamawa, su kuma al'ummar jihar kowa ya fita harkokinsa kamar yanda su ka sa ba gabatarwa yau da kullum.

Mutane sun ki fita wurin zabe a jihar Adamawa
Mutane sun ki fita wurin zabe a jihar Adamawa
Asali: UGC

Majiyarmu LEGIT.NG ta samu rahoton cewa masu shaguna sun fito kowa ya bude shagonshi, haka ma ababen hawa kowa yana ta harkokinsa kamar ba ranar zabe ba.

KU KARANTA: Akwai yiwuwar a sake sabon zaben shugaban kasa a Najeriya

Idan ba a manta ba hukumar zabe ta dakatar da zaben gwamnan jihar, bayan samun zaben da ta yi da kura-kurai.

A zaben da ya gabata na ranar 9 ga watan Maris, dan takarar jam'iyyar PDP ne ke kan gaba da kuri'u 367,471, inda shi kuma dan takarar jam'iyyar APC ke da kuri'u 334,995.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel