Saurayi ya kashe Budurwar sa a jihar Ondo

Saurayi ya kashe Budurwar sa a jihar Ondo

Hukuncin na shari'a mai tattare da adalci ya kan farantawa wadanda aka zalunta yayin da ya ke kasancewa kishiyar haka musamman ga 'yan uwa, makusanta, abokanan arziki da kuma dangin wadanda akan kwaci hakki a hannun su.

Shekaru uku da suka gabata, Chukwudi Onweniwe, wani dalibin makarantar gaba da Sakadandire ta Rufus Giwa dake jihar Ondo, ya kashe Budurwar sa, Nifemi Adeyeoye bayan ya yi ma ta fyade a wata gona dake yankin Ogbese a karamar hukumar Akure ta Arewa.

Saurayi ya kashe Budurwar sa a jihar Ondo
Saurayi ya kashe Budurwar sa a jihar Ondo
Asali: UGC

A ranar 22 ga watan Mayun 2017, Onweniwe ya gurfana gaban babbar kotun dake zamanta a birnin Akure inda ya amsa laifin sa tare da shaidawa jami'an tsaro cewa nishadi ya sanya ya aikata wannan ta'addanci.

Onweniwe ya bayyana yadda shekaru uku da suka gabata ya yiwa Budurwasa ta karfi zuwa wata gona mallakin Mahaifan sa inda bayan ya biya bukatar sa ta sha'awar da namiji ya kuma makure ta har sai da ta daina numfasawa.

KARANTA KUMA: Mayakan Boko Haram sun kai hari garin Chibok da Madagali

A yayin alakanta laifin sa da sharrin Shaidan tare da neman sassauci na hukuncin Kotun, Alkali Samuel Bola ya yankewa Onweniwe hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan da shaidu da kuma jami'in dan sanda mai shigar da kara, Jumoke Ogunjebi ya fayyace girman laifin da ya aikata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel