Mayakan Boko Haram sun kai hari garin Chibok da Madagali

Mayakan Boko Haram sun kai hari garin Chibok da Madagali

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, al'ummar Madagali da Michika sun tsere daga yankunan su yayin da kungiyar masu tayar da kayar baya na Boko Haram suka zartar da wasu munanan hare-hare na kisan rayuka da kone muhallai.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, daruruwan mutane da harin ya shafi kauyukan sun tsere muhallan su tare da yin hijira wajen neman mafaka a garuruwan Gulakda kuma Mubi da makotaka da su.

Rahotanni sun bayyana cewa, A daren Asabar Mayakan Boko Haram sun salwantar da dukiya mai tarin yawa a kauyen Kuda-Kaya yayin wani bakin gumurzu tsakanin su da dakarun kungiyar sa kai da 'yan Bijilanti.

Mayakan Boko Haram sun kai hari garin Chibok da Madagali
Mayakan Boko Haram sun kai hari garin Chibok da Madagali
Asali: Depositphotos

Wannan mugun ji da mugun gani ya biyo bayan aukuwar wani mummunan hari makamancin sa akan iyakar jihar Borno da Adamawa inda rai guda ya salwanta ba ya ga kone gidaje a kauyen Gatamarwa dake garin Chibok a ranar Alhamis.

Kazalika a ranar Laraba kauyen Hantsa dake garin Madagali ya fuskanci wani mummunan hari na Mayakan Boko Haram inda rai guda na daya daga cikin 'yan ta'adda ya yi halin sa yayin da dakarun tsaro suka mayar da martani.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Shugaba Buhari ya gana da shugabannin tsaro na Najeriya

Yayin sabunta hare-haren su, Mayakan Boko Haram sun kashe wani mutum guda tare da kone gidaje da kuma shaguna fiye da 50 a garin Kopa-Mai-Kadiri na jihar Borno da kuma Kopa-Adamawa da ke kan iyakar birnin Yola.

Wani daga cikin masu neman mafaka, Garba Ayuba, ya shaidawa manema labarai cewa, ya rasa dukkanin wata dukiya da ya mallaka kazalika akwai mafi girman rashin kwanciyar hankali a kauyen su yayin da a halin yanzu ya samu tsira a garin Gulak.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel