Ka inganta jin dadin rayuwar al'ummar Najeriya a wa'adin ka na biyu - Tinubu ya shawarci shugaba Buhari

Ka inganta jin dadin rayuwar al'ummar Najeriya a wa'adin ka na biyu - Tinubu ya shawarci shugaba Buhari

Babban jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, a ranar Alhamis ya yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari kashedi kan tafarkin da ya kamata ya bi na tsare-tsaren gwamnatin sa a wa'adi na biyu.

Kanwa Uwar gamin matsalolin jam'iyyar APC, ya shawarci shugaban kasa Buhari akan jajircewa wajen dabbaka tsare-tsare na inganta jin dadin al'umma domin ciyar da Najeriya gaba tare da tuni na cika kudirin matakin gaba watau Next Level da ya tallata yayin yakin sa na neman zabe.

Ka inganta jin dadin rayuwar al'ummar Najeriya a wa'adin ka na biyu - Tinubu ya shawarci shugaba Buhari
Ka inganta jin dadin rayuwar al'ummar Najeriya a wa'adin ka na biyu - Tinubu ya shawarci shugaba Buhari
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan jihar Legas ya yi furucin haka yayin bikin murnar cikar sa shekaru 67 a duniya da aka gudanar cikin babban birnin kasar nan na tarayya. Ya yi gargadin cewa duk wani yunkuri da gwamnati ta nufaci aiwatar wa ya kasance ya na da manufa ta fidda kasar nan zuwa tudun tsira tare da habaka tattalin arzikin ta.

A yayin babban taron da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta a madadin shugaban kasa Buhari, Tinubu ya yi kashedin cewa yunkurin gwamnati na kara tsadar haraji ba zai haifar da komai ba face radadi na talauci akan al'umma.

KARANTA KUMA: Dogara ya zargi Buhari da laifin kawo tsaikon shigar da kasafin kudin kasa na 2019 cikin doka

Tinubu yayin shawartar shugaban kasa Buhari akan abin da ya dace ya aiwatar a kujerar sa ta mulki karo na biyu, ya yi kira kan kara kaimi da zage dantse wajen inganta ci gaban gine-gine da kuma habakar tattalin arzikin domin cimma kyakkyawar makoma a kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel