Dogara ya zargi Buhari da laifin kawo tsaikon shigar da kasafin kudin kasa na 2019 cikin doka

Dogara ya zargi Buhari da laifin kawo tsaikon shigar da kasafin kudin kasa na 2019 cikin doka

- Kakakin Majalisar wakilai ya zargin shugaban kasa Buhari da laifin kawo tsaikon shigar da kasafin kdun kasa na bana a kuma shekarun baya

- Yakubu Dogara ya ce shugaban kasa Buhari ya gabatar da kasafin kundin kasa na bana a ranar 19 ga watan Dasumba na 2018

- Dogara ya ce ba zai yiwau fadar shugaban kasa ta ci gaba da zargin 'yan majalisar tarayya da laifin haifar da tsaikon shigar da kasafin kudin kasa ba tare da la'akari da lokacin da ta gabatar da shi ba

Kakakin Majalisar Wakilai Honarabul Yakubu Dogara, ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da laifin kawo tsaikon shigar da kasafin kudin kasa na 2019 da kuma na shekarun baya ta hanyar rashin gabatar da su akan kari.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, Dogara cikin jawaban sa a zaman sauraron ra'ayi kan kasafin kudin kasa na 2019 ya ce, cikin shekarun da suka gabata fadar shugaban kasa na da kaso na laifi rashin gabatar da kasafin kudin kasa akan kari da hakan ke haifar da tsaikon shigar da shi cikin doka.

Dogara ya zargi Buhari da laifin kawo tsaikon shigar da kasafin kudin kasa na 2019 cikin doka
Dogara ya zargi Buhari da laifin kawo tsaikon shigar da kasafin kudin kasa na 2019 cikin doka
Asali: UGC

Ya ce tsawon shekarun kimanin uku da suka gabata Najeriya ta fuskanci kalubale na tsaikon shigar da kasafin kudin kasa cikin doka a sakamakon rashin gabatar da shi akan kari daga bangaren fadar shugaban kasa.

Dogara ya ce ba zai yiwu fadar shugaban kasa ta ci gaba da zargin Majalisar tarayya da laifin kawo tsaikon shigar da kasafin kudin kasa cikin doka ba tare da ta yi la'akari da na ta laifin ba na rashin gabatar da shi akan kari.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Buhari ta sa 'Yan a daidata sahu cikin layin masu cin fansho

A madadin gabatar da kasafin kudin kasa na 2019 a ranar 7 ga watan Nuwamban 2018, fadar shugaban kasa ta gaza inda ta gabatar da shi cikin zauren Majalisar tarayya a raar 19 ga watan Dasumban 2018 kamar yadda kakakin Majalisar ya bayyana.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Ministan Kudi, Zainab Ahmed, ta yi karin haske yayin zaman majalisar zantarwa a ranar Laraba da cewar gwamnatin za ta ci bashi domin tabbatar da kasafin kudin kasar nan na bana ya tafi akan tsari.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel