Gwamnatin Buhari ta sa 'Yan a daidata sahu cikin layin masu cin fansho

Gwamnatin Buhari ta sa 'Yan a daidata sahu cikin layin masu cin fansho

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis 28 ga watan Maris, ya kaddamar da wani sabon shiri na sanya masu neman na kansu ta hanyar sana'o'i da kuma cin gashin kai cikin tsarin masu cin fansho na gwamnatin tarayya.

Gwamnatin Buhari ta sa 'Yan a daidata sahu cikin layin masu cin fansho
Gwamnatin Buhari ta sa 'Yan a daidata sahu cikin layin masu cin fansho
Asali: Instagram

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya kaddamar da sabon shirin cikin fadar sa ta Villa da ke garin Abuja, inda ya bude shi ta hanyar yiwa wani mai sana'ar a daidata sahu, Sagir Shawa, rajistar farko da hannun sa.

Shugab a Buhari ya ce gwamnatin sa ta dabbaka wannan shiri ga al'ummar Najeriya masu cin gashin kai ta hanyar sana'o'i daban-daban domin samun madogara ta dan abin hannu a yayin da suka kwanta dama.

Ya yi kira na neman kungiyoyin masu sana'o'in hannu, 'yan kasuwanni da kungiyoyi masu zaman kansu da su yi riko da wannan sabon shiri hannu biyu biyu tare da bayar da hadin kai ga gwamnatin tarayya wajen wayar da kai ta fuskar alhinin da kuma romon da ke cikin sa.

KARANTA KUMA: Lauya ya yi barazanar maka Kamfanin NNPC a kotun kan daukan ma'aikata

Cikin wani rahoton mai nasaba da jaridar Legit.ng ta ruwaito, shugaban kasa Buhari a ranar Laraba ya jagoranci zaman majalisar zantarwa tare da mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo da kuma Ministoci 22 cikin babban dakin taro na Council Chambers da ke fadar Villa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel