An yanke wa wani malamin tsubbu shekaru 97 a gidan yari kan laifin zambar N5.6m

An yanke wa wani malamin tsubbu shekaru 97 a gidan yari kan laifin zambar N5.6m

Justice A.O. Otaluka na babban kotun Abuja da ke da zama a Apo, a ranar 27 ga watan Maris ta yanke wa Clement Joseph wanda aka fi sani da Dr. Omale hukuncin daurin shekaru 97 a gidan yari.

Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), ta fara gurfanar da shi karo na farko a ranar 7 ga watan Maris, 2017, bisa laifuffuka bakwai wanda ya hada da hadin baki don damfarar mutane kudi naira milyan 5,600,000.

Da wannan ne ta yanke masa hukuncin shekaru bakwai akan laifi daya ba tare da biyan kudin fansa ba da kuma yanke masa hukuncin shekaru 15 a kan kowanne laifi cikin laifuka shida da ya rage, wanda idan aka hada duka ya kama shekaru 97.

An yanke wa wani malamin tsubbu shekaru 97 a gidan yari kan laifin zambar N5.6m
An yanke wa wani malamin tsubbu shekaru 97 a gidan yari kan laifin zambar N5.6m
Asali: UGC

Dokar kurkuku ta tanadi dauri na lokaci guda, duk da haka zai share shekaru 13, ganin ya share shekaru biyu a kurkukun a baya.

Malamin tsubbun ya mayar wa wanda yayi wa damfara mai suna Bola Akintola naira miliyan 5.6 bayan roko daga lauyan mai gurfanarwa Elizabeth Alabi.

KU KARANTA KUMA: Dan marigayi Audu ya kaddamar da kudirinsa na takarar gwamna, ya sha alwashin kawo karshen yunwa

Ya damfari Akintola ne bayan yayi da’awan cewa yana da assirtaccen karfin kare ta daga hatsari na rayuwa.

Laifin ya ci karo da sashi 8(a) da 1(3) na dokar damfara da sauran laifuffuka na dokar 2006, kuma ya tanadi horo a sashi 1(3) a dokar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel