Hukumar INEC ta sa ranar da za a gudanar da zaben Jihar Ribas

Hukumar INEC ta sa ranar da za a gudanar da zaben Jihar Ribas

Hukumar zabe na kasa mai zaman kan-ta, INEC ta bayyana ranar da za ta cigaba da gudanar da zaben gwamna da ‘yan majalisun jihar Ribas. INEC ta sanar da wannan ne a jiya Ranar 27 ga Watan Maris.

INEC ta sanar da cewa za a gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokoki ne Ranar 2 ga Watan Afrilun gobe. Sabon jadawalin da aka fitar ya nuna cewa za a bayyana sakamakon zaben ne daga Ranar 2 zuwa 5 ga Watan Afrilu.

Kafin nan Hukumar ta INEC za ta gana da masu ruwa-da-tsaki a harkar zaben jihar a Ranar 30 ga Watan Afriku. INEC tace a Ranar 13 ga Watan Afrilu ne za a gudanar da duk wani zaben cike-gibi idan akwai bukatar yin hakan a jihar.

KU KARANTA: Abin da ya sa na sha kashi a zaben 2019 - Inji Gwamnan Bauchi

Hukumar INEC ta sa ranar da za a gudanar da zaben Jihar Ribas
INEC ta fara shirin tsaida sabon Gwamna a Jihar Ribas
Asali: Facebook

An dakatar da zaben jihar ne da aka shirya a ranar 10 ga Watan Maris a dalilin rikici da ya barke ko ta ina a jihar. Hukumar INEC ta gudanar da bincike inda ta gano cewa an yi amfani da jami’an tsaro har da soji wajen kawo rudani a zaben.

INEC tayi alkawarin cewa za ta yi zabe na gaskiya-da-gaskiya mai cike da adalci a farkon Wata mai zuwa kamar yadda ta tsara. Hukumar tayi kira ga mutanen jihar Ribas da su bada duk wani hadin-kai da ake bukata a lokacin wannan zabe.

Hukumar ta INEC mai zaman kan-ta tayi wannan bayani ne ta bakin wani babban Jami’in ta mai kula da harkar yada labarai da kuma wayar da kan jama’a game da zabe a jihar Ribas watau Edwin Enabor.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel