Dan marigayi Audu ya kaddamar da kudirinsa na takarar gwamna, ya sha alwashin kawo karshen yunwa

Dan marigayi Audu ya kaddamar da kudirinsa na takarar gwamna, ya sha alwashin kawo karshen yunwa

- Dan marigayi tsohon gwamnan jihar Kogi, Prince Mustapha Mona Audu, ya kaddamar da kudirinsa na takarar gwamna a zaben jihar da za a yi a watan Nuwamba

- Mustapha, wanda ya bayyana kudirinsa a bainar jama’a, yace zai yi takara ne a karkashin jam’iyyar Young Progressives Party (YPP)

- Ya sha alwashin kawo sauyi ga mawuyacin hali na yunwa, talauci, rashin biyan albashi da yawan mace-mace da ake yi a jihar

Prince Mustapha Mona Audu, dan marigayi tsohon gwamnan jihar Kogi, Prince Abubakar Audu, ya kaddamar da kudirinsa na takarar gwamna a zaben jihar da za a yi a watan Nuwamba.

Mustapha, wanda ya bayyana kudirinsa a bainar jama’a, a Lokoja yace zai yi takara ne a karkashin jam’iyyar Young Progressives Party (YPP).

Yace zai shiga tseren gwamnan ne domin kawo sauyi ga mawuyacin hali na yunwa, talauci, rashin biyan albashi da yawan mace-mace da ake yi a jihar.

Dan marigayi Audu ya kaddamar da kudirinsa na takarar gwamna, ya sha alwashin kawo karshen yunwa
Dan marigayi Audu ya kaddamar da kudirinsa na takarar gwamna, ya sha alwashin kawo karshen yunwa
Asali: Depositphotos

Mustapha yace zai gina kyakyawar gwamnati mai cike da kyawawan nufi, sannan ya kawo ci gaba wanda marigayi mahaifinsa ya tsara idan aka zabe shi a matsayin gwamna a watan Nuwamba.

Ya bukaci matasa da su hada hannu da shi wajen ganin mafarkinsa ya zamo gaskiya, inda ya kara da cewa Kogi zata daukaka idan har ya zama gwamna.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar NICreL tayi kaca-kaca da Faston da ya soki Gwamna El-Rufai

Har ila yau, Shugaban YPP na kasa, Bishop Amachri, ya bukaci mutanen jihar mussamman matasa, da su jadadda goyon bayansu ga jam’iyyar da yan takararta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel