Kungiyar NICreL tayi kaca-kaca da Faston da ya soki Gwamna El-Rufai

Kungiyar NICreL tayi kaca-kaca da Faston da ya soki Gwamna El-Rufai

- Wata kungiya ta nemi Chris Okafor ya bi a hankali da irin kalaman sa

- Wannan kungiya tace dole Okafor ya iya bakin sa saboda gudun fitina

- Faston yayi huduba kwanaki yana zargin El-Rufai da takurawa Kirista

Labari ya zo mana cewa wata kungiya mai suna New Initiative for Credible Leadership watau NICreL ta ja kunnen babban Limamin addinin kirista Fasto Chris Okafor da ya rika bi a hankali da kalaman sa idan yana so a zauna lafiya.

Babban Faston na Liberation City, yayi jawabi kwanaki a Ranar Lahadi inda yayi kir ga gwamnan jihar Kaduna watau Malam Nasir El-Rufai da ya daina gallazawa Kiristocin jihar. Faston yace gwamna El-Rufai ya tasa Kiristoci a gaba.

KU KARANTA: Raunin Gwamnati ya jawo ake garkuwa da mutane – Kiristocin Kaduna

Kungiyar NICreL tayi kaca-kaca da Faston da ya soki Gwamna El-Rufai
NICreL ta gargadi C. Okafor ya giji kawo abin da zai jefa mutane cikin rudani
Asali: Facebook

Kungiyar New Initiative for Credible Leadership tace irin wannan huduba da Faston yayi, yana iya jefa Najeriya gaba daya cikin rikicin addini. Wannan Fasto yace idan gwamnan na Kaduna bai janye shirin sa ba, Ubangiji zai yi fushi da shi.

Babban Fasto ya nemi gwamnatin Kaduna tayi maza ta janye kudirin kula da addini da ta kai gaban majalisar dokoki. Babban Darektan kungiyar NICreL, Samson Onwu, yace irin wadannan maganganu na iya zama barazana ga tsaron kasa.

Wannan kungiya mai zaman kan-ta, tace dole ayi tir da irin babatun da wannan Fasto ya fito yana yi. Samson Onwu ya gargadi Malamin addinin da ya guji amfani da sunan addini wajen dasa kiyayya da gaban addini da kabilanci a Kaduna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel