Dalilin da yasa za a fitar da shugaban majalisar dattawa daga arewa maso gabas

Dalilin da yasa za a fitar da shugaban majalisar dattawa daga arewa maso gabas

- Yankin arewa maso gabas suna kara samun goyon baya wurin fitar da shugaban majalisar dattawa a kasar nan

- Wata kungiya ta tabbatar da cewa babu yankin da suke da kwararrun Sanatoci kamar yankin arewa maso gabas

Wata kungiya a Najeriya ta bayyana wasu dalilai da ya sanya dole a fitar da shugaban majalisar dattawa daga yankin arewa maso gabas. Sanarwar wacce ta fito daga bakin shugaban kungiyar a jiya Laraba, 27 ga watan Maris, ya tabbatar da cewa akwai kwararrun Sanatoci, wadanda suka san kan aikin su a yankin na arewa maso gabas.

Dalilin da yasa za a fitar da shugaban majalisar dattawa daga arewa maso gabas
Dalilin da yasa za a fitar da shugaban majalisar dattawa daga arewa maso gabas
Asali: Facebook

Ya ce ba zai zabi daya a cikin su ba, amma ya kamata a gabatar da zabe domin fitar da wanda ya fi cancantaa cikinsu.

"Muna tsoron kada a sake maimaita irin abinda ya faru a gwamnatin baya, karkashin mulkin tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki. Kowa ya san da cewar matsalar da ta faru a baya ta yi wa gwamnantin baya illa ba kadan ba," in ji shugaban kungiyar.

KU KARANTA: Akwai yiwuwar a sake sabon zaben shugaban kasa a Najeriya

Ya kara da cewa, arewa ta tsakiya, ta yi mulkin shugaban majalisar dattawa na sama da shekara goma, saboda haka dole za a cire wannan yankin daga ciki, dan hakan shine zai tabbatar da adalci da zaman lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel