Daukan aiki: NNPC ta bayar da muhimmin sako ga wadanda suka tsallake matakin farko

Daukan aiki: NNPC ta bayar da muhimmin sako ga wadanda suka tsallake matakin farko

- Kamfanin NNPC ta kammala mataki na farko na tantance sabbin ma'aikatan da za ta dauka a 2019 ta shiga mataki na biyu na fitar da sunayen wadanda su kayi nasara tsallake matakin farko

- Kamfanin ya ce za a gayyaci wadanda su kayi nasarar tsallake matakin farko su zo domin rubuta jarabawar da za ayi ta hanyar amfani da komfuta

- Za a gudanar da jarabawar a wurare 50 a fadin Najeriya daga bisani za a gayyaci wadanda su kayi nasara domin yi musu wani gwajin na baka

Kamfanin mai na kasa NNPC ya ce ya kammala mataki na farko na tantance sabbin ma'aikatan da za a dauka a wannan shekarar ta 2019.

Babban manajan kamfanin, na sashin hulda da jama'a, Ndu Ughamadu ne ya sanar da hakan a ranar Laraba 27 ga watan Maris inda ya ce yanzu za su shiga mataki na biyu.

Legit.ng ta lura cewa kamfanin ya sanar ta shafinsa na Twitter mai lakabin @NNPCgroup cewa Ughamadu ya ce za a fitar da sunayen wadanda su kayi nasarar tsallake matakin farko.

Ya kara da cewa za a gayyaci wadanda su kayi nasara su zo domin sake rubuta wata jarabawar da za ayi ta hanyar amfani da na'ura mai kwakwalwa wato komfuta.

Idan ba a manta ba, a baya Legit.ng ta ruwaito cewa kamfanin na NNPC ta sanar da cewa za ta fara daukan sabbin ma'aikata kwanaki kadan bayan kammala babban zaben 2019.

NNPC ta bayar da sanarwar a shafukan sada zumunta inda ta bukaci masu sha'awa su tafi shafin intanet na kamfanin suyi rajista.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel