Jihohi kadan su ka ba maganar noma muhimmanci a Najeriya – Audu Ogbeh

Jihohi kadan su ka ba maganar noma muhimmanci a Najeriya – Audu Ogbeh

Ministan harkokin noma da raya karkara a Najeriya, Audu Ogbeh, ya bayyana cewa a cikin jihohin Najeriya 36 da ake da su, jihohi 11 kacal ne su ka dauki harkar noma da gaske a daidai wannan lokaci.

Cif Audu Ogbeh ya fadawa manema labarai cewa jihohi da-dama a kasar nan ba su dauki batun komawa harkar gona yadda ya kamata ba. Ministan ya kuma koka da matsalar da ake samu wajen amincewa da kasafin kudi a Najeriya.

Audu Ogbeh yake nuna cewa bata lokacin da ake yi a majalisar tarayya kafin a sa hannu a kan kundin kasafin kudin kasar yana da illa ga manoma domin kuwa a cewar sa, tun farkon shekara ya kamata a fara shiryawa aikin damina.

Ministan yace bai kamata ace sai an fara ganin ruwan sama, sannan za a fara tanadin aikin gona ba. Sai dai a kan samu matsala a majalisa kafin ayi na’am da kasafin kudin da aka gabatar wanda ke sa har ruwa ya sauko ba a shirya ba.

KU KARANTA: An yi dogon zama tsakanin Gwamnati da Malaman Jami’ian Najeriya

Jihohi kadan su ka ba maganar noma muhimmanci a Najeriya – Audu Ogbeh
Wasu Jihohi ba su komawa noma gadan-gadan ba inji Ogbeh
Asali: Depositphotos

Ogbeh ya nuna cewa za su yi bakin kokari wajen ganin sun shawo kan wannan matsala da ake samu game da kasafin kudin kasar wanda tun a bara aka mikawa ‘yan majalisa. Ya kamata ace dai yanzu an fara raba iri da sauran kayan noma.

Ministan ya lissafo kadan daga irin nasarorin da aka samu a harkar noma a Najeriya a gwamnatin nan inda yace an tura wasu Ma’aikatan N-Power zuwa Kauyuka a matsayin Malaman gona. Sannan kuma an kawo tsare-tsare irin su AIMMS da GES.

Babban Ministan yace bayan cikas din da Majalisa ke kawowa, ana yawan samun matsaloli ne a kasar, saboda mafi yawancin jihohi ba su tashi tsaye wajen maida hankali a bangaren noma a Najeriya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel