Takarar kujerar DSP: Sanatoci 56 suna goyon baya na - Kalu

Takarar kujerar DSP: Sanatoci 56 suna goyon baya na - Kalu

Gabanin zaben shugabanin majalisa tarayya karo na tara, tsohon gwamnan jihar Abia kuma zababen Sanata mai wakiltan Abia ta Arewa, Cif Orji Uzor Kalu ya ce zai shiga sahun masu takarar kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa wato deputy senate president, DSP.

Ya ce zai mutunta matakin da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta dauka na mika kujerar shugabancin majalisar zuwa yankin Arewa maso Gabas.

A zantawar da ya yi da manema labarai a ranar Laraba a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed (MMIA), Kalu ya ce idan za ayi adalci ya kamata a bari yankin Kudu maso Gabas su fitar da mataimakin shugaban majalisa.

Ya kuma yi alkawarin zai yi aiki domin tabbatar da inganta rayuwar 'yan Najeriya inda ya ce yiwa al'ummar Najeriya ne hidima ne babban abinda ya sa a gaba.

DUBA WANNAN: Diyar Ganduje tayi kaca-kaca da masu sukar mahaifinta a Tuwita

Takarar kujerar DSP: Sanatoci 56 suna goyon baya na - Kalu
Takarar kujerar DSP: Sanatoci 56 suna goyon baya na - Kalu
Asali: UGC

Sai dai ya yi barazanar yin takarar kujerar shugabancin majalisar idan jam'iyyar ba ta amince ta bawa yankin Kudu maso Gabas damar fitar da mataimakin shugaban majalisar dattawan ba.

Tsohon gwamnan ya ce ya ji kishin-kishin cewa jam'iyyar za ta bawa yankin Arewa maso Yamma kujerar mataimakin shugaban majalisar.

Kalu ya ce zai sanar da shugabanin majalisa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari matsayinsa duba da cewa Shugaba Buhari ya mayar da hankali wurin kwato wa Kudu maso Gabashin Najeriya hakkinsu.

Ya ce mikawa yankin Kusu maso Gabas kujerar mataimakin shugaban majalisar zai nuna wa yankin cewa ana damawa da su inda ya ce a yanzu akwai Sanatoci 56 da ke goyon bayansa.

"Idan za ayi adalci, Sai a fitar da shugaban majalisar da Arewa maso Gabas mataimakinsa kuma da Kudu maso Gbas. Shugaban jam'iyyar ya fito ne daga Kudu maso Kudu, Shugaban kasa daga Arewa maso Yamma, mataimakinsa daga Kudu maso Yamma, Shugaban majalisa kuma zai fito ne daga Arewa maso Gabas, 'yan majalisa za su zaba tsakanin Lawan da Ndume.

"Na samu labarin an bawa Arewa maso Yamma kujerer mataimakin shugaban majalisa, wannan bai dace ba. Ba zamu amince da hakan ba. Abokan aiki na suna tare da ni. Zan anye daga takarar shugabancin majalisa in koma na mataimakin shugaban majalisa saboda ina girmama jam'iyyar," inji Kalu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel