Ku daina duk wani bincike a kai na – Oshiomhole ya roki Kotu

Ku daina duk wani bincike a kai na – Oshiomhole ya roki Kotu

A jiya 27 ga Watan Maris ne Shugaban jam’iyyar APC mai mulki, Kwamared Adams Oshiomhole, ya nemi babban kotun tarayya da ke zama a Garin Abuja da tayi watsi da karar sa da aka kawo mata.

Adams Oshiomhole ya maida martani a kan shari’ar da ake nema ayi tsakanin sa da Bishof Osadolor Ochei. Wannan Malami kuma mai fafutukar gwagwarmaya yana zargin Oshiomhole da aikata ba daidai ba a lokacin yana gwamnan Edo.

Terhemba Gbashima, wanda shi ne Lauyan shugaban jam’iyyar APC ya fadawa kotu cewa karar sa da Osadolor Ochei ya kawo ba ta da matsaya a shari’a. Lauyan yace an shigar da kara kotu ne watanni 18 bayan zargin aikata wannan laifi.

Babban Lauya Gbashima yace ya kamata ace an maka tsohon gwamnan zuwa Kotu a lokacin da ake zargin sa da aikata wannan laifi ko kuma kamar bayan watanni 3. A bisa dalilin haka ne dai Lauyan ya roki Alkalin yayi watsi da karar.

KU KARANTA: Ya aka iya : APC ta amince da karashen zaben jihar Adamawa

Ku daina duk wani bincike a kai na – Oshiomhole ya roki Kotu
Shugaban APC Oshiomhole ya nemi a tsaida shari’ar sa
Asali: UGC

Ita kuma Lauyan mai kara mai suna Uju Chukwurah, ta nemi Alkali Anwuli Chikere, ya cigaba da bincike. Chukwurah ta nunawa kotu cewa abin da Lauyan wanda ake tuhuma yake dogoro da shi don yin watsi da karar, sam ba gaskiya bane.

Chukwurah ta kuma fadawa Alkali mai shari’a Anwuli Chikere cewa ainihin wanda ya shigo da wannan kara gaban kuliya watau Osadolor Ochei mutumin jihar Edo ne inda Oshiomhole ya fito don haka tace yana da damar shigar da kara a Kotu.

A kwanakin baya ne Bishof Osadolor Ochei ya kai tsohon gwamnan na Jihar Edo Adams Oshiomhole zuwa kotu inda yake nema a tursasawa hukumar EFCC da ta binciki wasu zargi da ke kan sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel