Ban karbi rancen kudi daga banki ba - Okorocha

Ban karbi rancen kudi daga banki ba - Okorocha

Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya ce gwamnatinsa ba ta karbo rancen kudi ba daga banki na gida Najeriya ke kasasahen waje ba.

Ya kuma musanta cewa babu wata banki ko dan kwangila da ke bin gwamnatinsa bashi.

A sanarwar da ya fitar a ranar Laraba 27 ga watan Maris a garin Owerri, Okorocha ya kallubalanci dukkan wani banki da ke ikirarin ya karbi bashi a wurinsa ya nuna wa duniya shaidan cewa akwai bashi tsakaninsu.

Gwamnan na Imo ya sha musanta zargin cewa ya jefa jihar a cikin bashi ya kallubalanci masu yin wannan zargin su bayyanawa duniya sunan bankin da adadin kudin da ya karbo bashin.

DUBA WANNAN: Diyar Ganduje tayi kaca-kaca da masu sukar mahaifinta a Tuwita

Ban karbi rance daga banki ba - Okorocha
Ban karbi rance daga banki ba - Okorocha
Asali: UGC

Ya ce: "Mun dauki wannan matakin ne saboda jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP sun saba karya da yada farfaganda.

"Idan kuma sun san bankin da Okorocha ya tafi ya karbi bashi ko da na naira daya ne, sai su fadi bankin tare da bayyana bayyanai a kan bashin saboda duk wani da ke sha'awar bincike a kan batun ya tabbatar da gaskiya. Idan kuma ba za su iya aikata hakan ba abinda ya fi dacewa shine suyi shiru da bakinsu."

"Kowa ya sani cewa wannan gwamnatin ta kasance tana bawa yara ilimi kyauta tun 2011 tun daga frimare har zuwa makarantun gaba da sakandire babu yaron da ke biyan ko kwabo daya a matsayin kudin makaranta kuma gwamnatin ta sake sayo kamfanonin gwamnatin jiha da gwamntocin baya suka sayar misali kamfanin fainti na Mbaise," inji sanarwar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel