Farfesa Zulum: Sabon gwamnan jihar Borno ya bayyana yadda zai tunkari matsalar BH

Farfesa Zulum: Sabon gwamnan jihar Borno ya bayyana yadda zai tunkari matsalar BH

Farfesa Babagana Umara Zulum, zababben gwamnan jihar Borno, ya ce gwamnatin sa zata bayar da fifiko ne wajen magance tushen matsalar da ta haifar da aiyukan ta'addanci da sunan kungiyar Boko Haram.

Zulum ya bayyana cewar ta wannan hanyar ne kadai za a iya shawo kan matsalar Boko Haram da ta shafe tsawon shekaru goma a jihar Borno.

Ya bayyana hakan ne bayan karbar takardar shaidar cin zabe da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta bashi a ranar Laraba, 27 ga watan Maris.

Zababben gwamnan ya karbi takardar shaidar tare da mataimakin sa, Usman Kadafur, da ragowar mambobin majalisar dokokin jihar Borno su 28.

Zulum ya bayyana cewar zai bayar da fifiko wajen sake bijiro da aiyuka ma tsare-tsare da zasu gaggauta kawo zaman lafiyar da zai bawa jama'a a jihar damar komawa gidajen su.

Farfesa Zulum: Sabon gwamnan jihar Borno ya bayyana yadda zai tunkari matsalar BH
Farfesa Babagana Zulum
Asali: Getty Images

Zulum ya ce, "gwamnati na zata bijiro da tsare-tsare nagari da zasu magance tushen rikicin Boko Haram, zamu samar da aiki ga matasa, zamu dawo da da'a da gyara mu'amala a tsakanin al'umma.

"Ina neman hadin kan zababbun mambobin majalisa dokoki domin hada karfi wajen ciya da jihar mu gaba."

DUBA WANNAN: Yadda PDP ta ci zaben gwamnan Sokoto da tazara ma fi karanci a tarihi

Da yake mika takardar shaidar ga wadanda aka zaba, AVM Ahmed Mu'azu (mai ritaya), ya bayyana cewar doka ce ta wajabta wa INEC bawa duk wanda aka zaba shaidar cewar ya ci zabe, kamar yadda yake a karkashin sashe na 75 na kundin dokokin zabe.

Mu'azu ya yi kira ga zababben gwamnan da ragowar wakilan da su sauke nauyin da ya rataya a wuyan su domin kawo cigaba a jihar su da kasa baki daya.

Kazalika ya yaba wa ma'aikatan zabe, hukumomin tsaro, jam'iyyu, kungiyoyin sa-ido da ragowar masu ruwa da tsaki da suka taka rawa wajen gudanar da zabe cikin nasara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel