'Yan bindiga sun kai wa shugaban NUJ hari, sun yi awon gaba da matar sa da wasu mata 3

'Yan bindiga sun kai wa shugaban NUJ hari, sun yi awon gaba da matar sa da wasu mata 3

Wasu 'yan bindiga sun kai wa shugaban kungiyar 'yan jarida (NUJ) reshen jihar Nasarawa, Suleiman Abubakar, hari tare da yin awon gaba da matar sa da, Yahanasu Abubakar.

Suleiman ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewar lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar Laraba, 27 ga watan Maris, a kan hanyar Gudi zuwa Garaku a karamar hukumar Akwanga dake jihar Nasarawa.

A cewar Suleiman, 'yan bindigar sun harbi motar kungiyar NUJ a kan hanyar zuwa kai matar sa sansanin bawa matasa 'yan bautar kasa (NYSC) horo dake Keffi.

Ya kara da cewar bayan motar ta fada cikin wani rami, 'yan bindigar sun yi awon gaba da matar sa da matar wani tsohon dan majalisar dokokin jihar Nasarawa da suka rage wa hanya da kuma wasu mata biyu daga cikin wata motar daban da tsautsayi ya kawo ta a daidai lokacin da 'yan bindigar ke cin karen su babu babbaka.

'Yan bindiga sun kai wa shugaban NUJ hari, sun yi awon gaba da matar sa da wasu mata 3
'Yan bindiga sun yi awon gaba da matan aure a jihar Nasarawa
Asali: Facebook

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa (PPRO), ASP Samaila Usman, ya ce rundunar 'yan sanda ta baza jami'anta zuwa yankin da abin ya faru domin kubutar da matan da aka sace, kamar yadda NAN ta rawaito.

A wani kabarin na Legit,ng daga jihar Nasarawa, kun ji cewar an kashe mutane biyu tare da kone gidaje 38 a wani rikicin kabilanci da ya barke a garin Andaha da ke karkashin hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace dan asalin kasar Koriya ta Arewa a Zamfara

Mazauna kauyuka uku da ke kusa da garin da rikicin ya faru sun kaurace wa gidajen su saboda tsoron kai harin daukan fansa a kan su. Mutanen sun fara kauracewa gidajen su ne bayan samun rahoton kashe wata budurwa mai shekaru 19 da ake zargin wasu makiyaya da aikata wa.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Nasarawa, Samaila Usman, ya tabbatar da afkuwar rikicin ga gidan Talabijin na Channels a hirar su da shi ta wayar tarho.

A cewar sa, rikicin ya samo asali ne bayan wasu da ake zargin makiyaya ne sun yiwa wasu mata uku 'yan kabilar Mada fyade yayin da suke dawowa daga wurin wani biki da suka halarta a garin Katanza.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel