Yanzu-yanzu: Boko Haram sun kai hari kan Masallata a Borno

Yanzu-yanzu: Boko Haram sun kai hari kan Masallata a Borno

Yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram sun kai kari garin Miringa, karamar hukumar Biu dake jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa yan ta'addan sun dira cikin garin ne misalin karfe 6:30 na yamma yayinda jama'a suke Sallar Magariba inda suka fara harbe-harben bindiga da roka.

Yan ta'addan sun kai hari barikin Soji inda suka kashe jami'in dan sanda daya da mazauni garin daya, idanuwan shaida sun bada rahoto ranar Alhamis.

Mayakan Boko Haram sun dira garin cikin motoci 13 inda suka kona barikin sojin kuma suna bankawa wata makarantar firamare wuta.

Idon shaidan mai suna Umar Sanda ya bayyanawa AFP cewa: "Sun iso misalin karfe 6:30 na yamma cikin motoci 13 kuma suka kai hari inda Soji suke a wajen garin."

"Sai da aka kwashe sama da awa 1 suna musayar wuta yayinda mutanen kauyen suka gudu cikin daji."

Wani mazauni mai suna Abba Usman ya bayyana cewa daga baya suka dawo muhallansu suka tarar an kona barikin sojin, masaukin sojin, mota, da kuma wani sashen makarantar firamare.

An kasance ana kai hari garin Miringa tun lokacin da babban hafsan sojin Najeriya, Buratai, ya hau mulki a 2015.

A watan Junairun 2019, an hallaka soji 6 kuma 14 sun jikkata a harin da Boko Haram ta kai barikin soji a kauyen Kamuya inda suka sace makaman soji.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel