Daga karshe, jam'iyyar APC ta amince da cikamakin zaben jihar Adamawa

Daga karshe, jam'iyyar APC ta amince da cikamakin zaben jihar Adamawa

Jam'iyyar All Progressives Congress ta yi kira ga magoya bayanta su shirya tsaf domin musharaka a zagayen zabe na biyu da hukumar gudanar da zabe ta kasa mi zaman kanta ta sanya ranar Alhamis, 28 ga watan Maris, 2019.

Sakataren shirye-shiryen jam'iyyar, Alhaji Ahmed Lawal, ya bada umurnin ne ranar Laraba, a hirarsa da kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN.

Lawal ya ce jam'iyyar ta canza ra'ayinta kan maganar da tayi na farko na kin amincewa da cigaba da zaben da kuma barazanar kin musharaka a zaben.

Ya ce duk da rashin sauraronsu da hukumar INEC tayi, za su samu nasara a zaben. Ya yi kira ga yan jam'iyyar APC su fito kwansu da kwarkwatansu su zabi dan takarar jam'iyyar.

KU KARANTA: Ban yi jima'i da ita ba, wasa kawai nayi - Likitan da akayiwa zargin fyade matar aure ya yi magana

Yace: "Bayan shawarwari da mukayi da masu ruwa da tsakin jam'iyyar, mun yanke sharar musharaka cikin cikamakin zaben da za'a yi gobe (Alhamis)."

"Kokarin kauracewa zaben da mukayi niyyar yi a baya ba tsoro bane, amma don taimakawa saura jam'iyyu wajen musharaka."

"Amma mu, za muyi musharaka duk da cewa INEC ta ki canza ra'ayinta kan zaben gobe. Muna kira ga masoya APc su fito kwansu da kwarkwatarsu su zabi APC."

"Adamawa jihar APC ce, da irin ayyukan cigaban da gwamna Mohammed Bindow yayi, ya tabbatar cewa zai samu nasara a zaben." Lawal yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel