Dalilin mu na son Sanata Lawan ya zama shugaban majalisar dattijai - APC

Dalilin mu na son Sanata Lawan ya zama shugaban majalisar dattijai - APC

'All Progressive Congress (APC)' ta bayyana cewar ta yanke shawar tsayar da Sanata Ahmed Lawan a matsayin wanda take so ya zama sabon shugaban majalisar dattijai bayan tuntubar shugabanni da kuma ragowar masu ruwa tsaki a harkokin jam'iyyar.

APC ta bayyana cewar ta yanke shawarar mamaye dukkan mukaman majalisar tarayya ne saboda ita ce keda mafi rinjayen mambobi a zauren majalisar.

Da yake tattauna wa da manema labarai a Abuja, sakataren yada labaran jam'iyyar APC na kasa, Mallam Lanre Issa-Onilu, ya bayyana cewar APC ta zabi Sanata Lawan a matsayin wanda take so ya zama shugaban majalisar dattijai domin samun daidaito a rabon mukaman majalisar wakilai da ta dattijai, wanda hakan ya hada da mukaman shugabannin majalisar tarayya.

Onilu ya kara da cewa APC na sane da cewar akwai ragowar Sanatocin dake son kujerar shugabancin majalisar, tare da bayyana cewar jam'iyyar APC na da manyan sanatoci daga kowanne yanki na kasar nan da suke da nagartar neman kujerar shugabancin majalisar, amma mutum daya ne a karshe zai zama shugaban majalisar.

Dalilin mu na son Sanata Lawan ya zama shugaban majalisar dattijai - APC
Sanata Ahmed Lawan
Asali: Depositphotos

Ya kara da cewa jam'iyyar APC ba zata yi sake abinda ya faru a shekarar 2015 a majalisar dattijai ya maimaita kan sa ba wannan karon.

Kazalika, Jam'iyyar ta fito fili ta bayyana cewar ba zata iya taimakon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ba kamar yadda ta yanke shawara a baya.

DUBA WANNAN: Yaba kyauta: Ganduje ya ziyarci mazabar Gama, ya basu tukucin aikin N12m

Jam'iyyar ta bayyana cewar ba zata janye shawarar da ta yanke na kin saka baki ba a kan matsalar da Rochas ke fuskanta da hukumar zabe ta kasa (INEC) ba har sai dakatar war da ta yi masa ta kare.

Da yake magana a kan rashin bawa Okorocha takardar shaidar cin zaben kujerar sanata da INEC tayi, Onilu ya ce, "ba zamu dauki wani mataki a kan batun ba. Mun dakatar da Rochas tuntuni, kuma shi ma bai zo mana da korafi ko bukatar mu saka baki a kan matsalar sa da INEC ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel