Ban yi jima'i da ita ba, wasa kawai nayi - Likitan da akayiwa zargin fyade matar aure ya yi magana

Ban yi jima'i da ita ba, wasa kawai nayi - Likitan da akayiwa zargin fyade matar aure ya yi magana

Tijjani Farouk, likitan asibiti a jihar Sokoto wanda akayiwa zargin yiwa matar aure allurar bacci sannan yayi mata fyade ya furta albarkacin bakinsa gaban kwamitin binciken da ma'aikatar lafiyan jihar ta nada.

A wata maganar rediyo, Likitan ya amsa cewa ya aikata laifin amma bai take ta ba, innama wasa kawai yayi da jikinta.

Yace: "A iyakan sani na, lokacin da ta shigo dakin ranar Asabar ne, tare da wata karamar Yarinya. Inada abin cewa a nan. Ina son a share wannan maganar. Maganar gaskiya shine mun yi jima'i da Zuwaira. Na amince"

Amma lokacin da mambobin kwamitin binciken suka fada masa illar abinda ya fada zai yi masa, sai ya lashe amansa, ya ce sun yi wasan soyayya amma bai ratsata ba.

"Ban yiwa Zuwaira fyade ba. Na rantse da Allah, ina fada muku hakan ne saboda dukkanmu maza ne. Zuwaira ta zo wajen ba sau daya ba, ba sau biyu ba." Yace

KU KARANTA: Yadda muka ceto Alaramma Ahmed Suleiman da mukarrabansa - Hukumar Soji

Mun kawo muku rahoton cewa Wani Likita a asibitin gwamnati dake jihar Sokoto mai suna, Tijjani Faruk, ya tayar da hankalin jama'ar asibitin bayan tona asirin kansa cewa ya yiwa wata matar aure mai jinya fyade bayan tsira mata alluran barci.

A wata hira da jaridar Daily Nigerian tayi da mijin matar da abin ya auku da ita mai suna Alhaji Shehu, ya bayyana cewa wani abokinsa ne ya basu shawaran zuwa wajen Likitan yayinda aka gano tanada wasu kulli a mararta wanda akafi sani da "Fibroid".

Watanni bayan aikin tiyata da aka gudanar domin cireshi, sai Likitan ya kirashi a waya cewa yana bukatar ganin matarsa domin akwai wasu dube-dube da yake bukatan yi mata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel