Malaman Jami’a sun koma kan tebur da Gwamnatin Najeriya domin gyara harkar ilmi

Malaman Jami’a sun koma kan tebur da Gwamnatin Najeriya domin gyara harkar ilmi

Labari ya zo mana daga manema labarai a yau dinnan cewa Gwamnatin Najeriya ta koma cigaba da zama da kungiyar ASUU ta manyan Malaman jami’o’in gwamnati domin duba yarjejeniyar da aka yi a 2009.

Dr Wale Babalakin wanda shi ne shugaban kwamitin da Gwamnatin tarayyar Najeriya da kafa domin zama da kungiyar ASUU ya bayyana cewa sun yi zama da Malaman makarantar gwamnati a Ranar Laraba 27 ga Watan Maris.

Wale Babalakin, a madadin gwamnati yake cewa sun yi akalla sa’a 6 su na tattaunawa da Wakilan kungiyar ASUU a babban birnin tarayya Abuja. Babalakin ya kuma bayyana cewa sun tattauna game da batutuwa fiye da 20 a zaman.

KU KARANTA: Babban Malami Ahmad Sulaiman ya baro hannun ‘Yan bindigan da su ka tsare sa

Malaman Jami’a sun koma kan tebur da Gwamnatin Najeriya domin gyara harkar ilmi

An yi wani zama na gemu-da-gemu da Gwamnati da Malaman Jami’a
Source: Depositphotos

Wakilin gwamnatin tarayyar yake fadawa manema labarai dazu cewa malaman jami’o’in kasar sun kawo duk manyan batutuwan da ya kamata a duba domin ganin an gyara makarantun jami’o’i na gwamnati da ke fadin Najeriya.

Babalakin ya bada tabbacin cewa dukkanin bangaren a shirye su ke da su ga an kawo karshen tabarbarewar harkar ilmin jami’o’i a Najeriya. Wale Babalakin ya nuna cewa zaman na su yana tafiya daidai kamar yadda su ke so.

Gwamnatin shugaba Buhari ta na sa ran cewa an kusa ganin karshen yajin aikin da Malamai ke yawan zuwa a makarantun jami’o’i. Kwanan nan ne ma aka bude makarantun kasar bayan wani dogon yajin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel