Ba zamu iya taimakon Rochas a kan matsalar sa da INEC ba - APC

Ba zamu iya taimakon Rochas a kan matsalar sa da INEC ba - APC

Jam'iyyar APC mai mulki ta fito fili ta bayyana cewar ba zata iya taimakon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ba kamar yadda ta yanke shawara a baya.

Jam'iyyar ta bayyana cewar ba zata janye shawarar da ta yanke na kin saka baki ba a kan matsalar da Rochas ke fuskanta da hukumar zabe ta kasa (INEC) ba har sai dakatar war da ta yi masa ta kare.

APC ta dakatar da Rochas tare da takwaransa Ibikunle Amosun, gwamnan jihar Ogun, bayan an same su da laifin goyon bayan 'yan takarar gwamna da ba na jam'iyyar APC ba a jihohin su.

Okorocha ya tsayar da surukinsa, Uche Nwosu, takarar gwamnan jihar Imo a karkashin jam'iyyar AA bayan ya fadi a zaben fidda 'yan takara na jam'iyyar APC.

Ba zamu iya taimakon Rochas a kan matsalar sa da INEC ba - APC
Rochas Okorocha
Asali: Twitter

A daya bangaren, Amosun ya goyi bayan dan takarar sa, Abdulkadir Akinlade, da ya tsayar a jam'iyyar APM bayan ya gaza cimma samun nasara a zaben fidda 'yan takara na jam'iyyar APC.

Dukkan gwamnonin biyu sun tsaya takarar kujerar sanata a jam'iyyar APC a yayin da suke goyon bayan 'yan takarar su na gwamna da suka a wasu jam'iyyun.

DUBA WANNAN: Yaba kyauta: Ganduje ya ziyarci mazabar Gama, ya basu tukucin aikin N15m

Sai dai INEC ta ki bayar da takardar shaidar cin zabe ga Rochas a lokacin da ta raba takardun shaidar ga zababbun 'yan majalisar tarayya ('yan majalisar wakilai da na dattijai).

Da yake magana a kan rashin bawa Okorocha takardar shaidar da INEC tayi, Lanre Issa-Onilu; sakataren yada labaran jam'iyyar APC, ya ce, "ba zamu dauki wani mataki a kan batun ba. Mun dakatar da Rochas tuntuni, kuma shi ma bai zo mana da korafi ko bukatar mu saka baki a kan matsalar sa da INEC ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel