Yaba kyauta: Ganduje ya ziyarci mazabar Gama, ya basu tukucin aikin N12m

Yaba kyauta: Ganduje ya ziyarci mazabar Gama, ya basu tukucin aikin N12m

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ziyarci mazabar Gama dake karkashin hukumar Nasarawa a cikin birnin Kano domi yi masu godiya a kan kuri'un da suka zazzaga masa yayin zaben raba na ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

Tun bayan da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta sanar da cewar sai an gudanar da zaben raba gardama a jihar Kano sunan mazabar Gama ya shiga bakin duniya saboda yawan adadin kuri'un mazabar da aka soke.

Gwamna Ganduje ya mayar da mazabar tamakar gidan gwamnati saboda yawan kai ziyara tare da kaddamar da muhimman aiyuka da raba jari ga mata da matasa a unguwar.

A cikin dan kankanin lokaci gwamna Ganduje ya gina tituna, ya haka rijiyoyin burtsatse, da sayen injin wutar lantarki a masallacin Sasif dake mazabar.

Yaba kyauta: Ganduje ya ziyarci mazabar Gama, ya basu tukucin aikin N15m
Ganduje ya ziyarci mazabar Gama
Asali: Twitter

Kamar yadda Hausawa ke cewa 'yaba kyauta ke sa a bayar da tukuci', gwamna Ganduje ya kara komawa mazabar ta Gama a yau, Laraba, domin yi masu godiya a kan fitowar da suka yi suka zazzaga masa kuri'a a zaben raba gardama da aka gudanar ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

DUBA WANNAN: Ba da tashin hankali na ci zabe ba; Ganduje ya fadi sirrin samun nasarar sa

A yayin ziyarar ta sa, gwamnan ya kara koma wa masallacin na Sasif inda ya sayi wani gida mai makobtaka da masallacin a kan kudi har miliyan N15 domin a fadada harabar masallacin.

Sai dai jama'a d dama sun soki gwamnan a kan irin aiyukan da ya yi a mazabar ta Gama, su na masu fadin cewar ba don Allah ya yi ba, sai don samun kuri'un jama'ar mazabar.

Da yake kare kan sa, Ganduje ya ce ba a makara da aikata alheri, tare da bayyana cewar dama yana da niyyar yiwa unguwar aiyuka amma sai yanzu Allah ya kawo lokacin gudanar da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel