Hukuncin kotun karar zabe: Masu zanga-zanga sun mamaye babban birnin jihar Osun

Hukuncin kotun karar zabe: Masu zanga-zanga sun mamaye babban birnin jihar Osun

A halin yanzu ana gudanar da zanga-zanga a garin Osogbo babban birnin jihar Osun a kan hukuncin da kotun kararrakin zabe ta yanke na kwace nasara daga hannun dan takarar gwamna na APC, Gboyega Oyetola ta mika wa Ademola Adeleke na PDP.

Masu zanga-zangan da suka taru a karkashin kungiyar Osun Concerned Citizens sun fito dauke da takardu da rubuce-rubuce da ke nuna rashin jin dadinsu game da hukuncin ta kotun ta yanke.

Premium Times ta gano cewa an fara zanga-zangar ne misalin karfe 12 na rana a mahadar Ayetoro kuma a lokacin da ake rubuta wannan rahoton sun nufi tsohuwar gareji da ke Osogbo.

DUBA WANNAN: Yadda kananan yara masu talla ke yada cutar Kanjamau a Borno

Hukuncin kotun karar zabe: Masu zanga-zanga sun mamaye babban birnin jihar Osun
Hukuncin kotun karar zabe: Masu zanga-zanga sun mamaye babban birnin jihar Osun
Asali: Twitter

Daya daga cikin masu zanga-zangar, Ismail Alamu ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa ya zama dole suyi zanga-zangar ne saboda su kwato nasasarsu da aka kwace.

"Ba zamu tsaya a nan ba. Zamu tafi Abuja mu nuna rashin jin dadin mu domin tabbatar da cewa kotun daukaka kara tayi adalci," inji shi.

A baya, jam'iyyar PDP reshen jihar Osun tayi zargin cewa APC na shirin daukan hayar masu zanga-zanga a kan hukuncin kotun sauraron karar zaben sai dai APC ta ce sharri ne.

A makon da ta gabata ne kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke hukuncin cewa Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP ne ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 22 ga watan Satumban 22.

Kotun ta ce zaben raba gardamar da akayi a ranar 27 ga watan Satumba ta sabawa doka sai dai Mr Oyetola ya garzaya kotun daukaka kara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel