Abubuwan da Buhari ya fada a kan Tinubu a sakon taya shi murnar cika shekaru 67

Abubuwan da Buhari ya fada a kan Tinubu a sakon taya shi murnar cika shekaru 67

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika sakon taya murna ga jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinu, yayin da ya cika shekaru 67 a duniya.

Shugaban kasar ya bayyana Tinubu a matsayin daya daga cikin ginshikan dake rike da siyasar Najeriya.

Buhari ya aike da sakon taya murnar ne ta bakin kakakin sa, Femi Adesina.

Shugaba Buhari ya jinjina wa Tinubu bisa sadaukar war sa ga jam'iyyar APC da kuma yaki da rashin adalci kamar yadda ya nuna a lokacin da aka soke zaben ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993, wanda a sakamakon hakan har sai da ya yi gudun hijira, ya bar Najeriya na tsawon wsu shekaru.

Abubuwan da Buhari ya fada a kan Tinubu a sakon taya shi murnar cika shekaru 67
Buhari da Tinubu
Asali: Twitter

"Shugaba Buhari ya tabbatar da cewar Tinubu ya zama daban a cikin ragowar 'yan siyasar Najeriya ne saboda hidimar sa ga dimokradiyya da kyamar da yake nuna wa ga rashin adalci da son rai.

"Tauraron sa a siyasa ya kara haska wa bayan ya zama gwamna a jihar Legas na tsawon shekaru 8, inda ya saka tubalin da ya mayar da Legas cibiyar kasuwanci da fasaha a Najeriya. Duk ragowar gwamnonin da suka mulki jihar a bayan sa na amfani da taswirar sa ta gina Legas a matsayin babban birni da za a yi alfahari da shi a kaf Afrika." a cewar jawabin da Adesina ya fitar.

DUBA WANNAN: Ma'aikata sun bawa FG shawarar yadda za ta samu kudin biyan sabon karin albashi

Jawabin ya kara da cewa shugaba Buhari ya shiga jerin sahun 'yan uwa, abokai na siyasa da kasuwanci wajen taya Tinubu murnar cika shekaru 67 a duniya. .

"Shugaba Buhari ya yi imanin cewar tauraron jagoran jam'iyyar APC zai ci gaba da haska wa a siyasar Najeriya, tare da yi masa addu'ar Allah ya yi masa nisan kwana cikin koshin lafiya ya kuma kara masa basira," a cewar jawabin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel