Zaben Adamawa: PDP ta fallasa wani kulli da APC ke yi na kai mamaya da yan daba

Zaben Adamawa: PDP ta fallasa wani kulli da APC ke yi na kai mamaya da yan daba

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Adamawa, ta zargi Shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki da kulla makirci na hayo yan iska daga Kano da Kaduna domin su tarwatsa zaben ranar Alhamis a jihar.

A wata sanarwa dauke da sa hannun Shugaban PDP a jihar, Barista Tahir Shehu a ranar Laraba, 26 ga watan Maris, yace jam’iyyar ta samu bayani game da shirin APC na kawo yan iskan domin su tarwatsa zaben.

“Amma mun samu bayani kuma mun yi amanna cewa gwamnatin APC a jihar Adamawa na ikirarin cewa Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, da Gwamna Ganduje na jihar Sokoto, sun yi alkawarin taimaka masu da yan iska domin su mamaye jihar Adamawa a kokarinsu na magudin zaben da za a sake don ganin sun yi nasara a kowani hali,” cewar jawabin.

Zaben Adamawa: PDP ta fallasa wani kulli da APC ke yi na kai mamaya da yan daba
Zaben Adamawa: PDP ta fallasa wani kulli da APC ke yi na kai mamaya da yan daba
Asali: Depositphotos

Sanarwar ya kuma shawarci masu zabe da su kwantar da hankalinsu sannan su tabbatar da cewar sun gudanar da hakkin da ya rataya a wuyansu na zabar dan takarar da suke muradi.

Da yake martani a nashi bangaren, sakataren APC a jihar, Muhammad Abdullahi, yace jawabin ya fallasa mugun nufin da PDP ke kullawa gabannin zaben.

KU KARANTA KUMA: Galadima yace lallai akwai ha’inci a sakamakon zaben Shugaban kasa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Adamawa, ta yi barazanar kaurace ma zaben gwamna da za’a sake idan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta dage cewan zata gudanar da zaben a ranar Alhamis, 2 ga watan Maris.

Sakataren tsare-tsare na jam’iyyar APC, Alhaji Ahmed Lawan, ya bayyana matsayar jam’iyyar a ranar Laraba, 26 ga watan Maris a Yola.

Lawan ya fada wa kamfanin Dillancin Labarai (NAN) cewa jam’iyyar ta nuna rashin amincewa da zabe a ranar Alhamis kuma ta sanar da hukumar zaben matsayin ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel