Rundunar sojin Najeriya ta ceto wata yar karamar yarinya daga hannun Boko Haram (hotuna)

Rundunar sojin Najeriya ta ceto wata yar karamar yarinya daga hannun Boko Haram (hotuna)

Tun jiya ake yada hoton wani jajirtaccen soja a shafukan zumunta yayin da ya ceto wata yar karamar yarinya daga kangin yan ta’addan Boko Haram.

Sojan wanda ba a san takamaiman sunan sa ba a dai dai lokacin hada wannan rahoton, ya ceto yarinyan mai suna Success, yayin da rundunar ke yakar yan kungiyan Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Success ta rasa iyayenta a lokacin yaki tsakanin rundunar sojin Najeriya da yan ta’addan.

Hakika rundunan sojin Najeriya na kokari wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma tsare rayukan yan Najeriya a kasar su.

Kalli hotunan a kasa:

Rundunar sojin Najeriya ta ceto wata yar karamar yarinya daga hannun Boko Haram (hotuna)
Yarinyar tare sojojin da suka ceto ta
Asali: UGC

Rundunar sojin Najeriya ta ceto wata yar karamar yarinya daga hannun Boko Haram (hotuna)
Rundunar sojin Najeriya ta ceto wata yar karamar yarinya daga hannun Boko Haram
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Rundunar yan sanda ta tabbatar da sakin Sheikh Ahmad Suleiman da wasu a Katsina

A wani lamari makamancin wannan, Legit.ng ta rahoto cewa hukumar sojin Najeriya ta bayyana yadda ta ceto babban malamin addini, Sheik Ahmad Suleiman, da mukarrabansa guda biyar da akayi garkuwa da su ranar 14 ga watan Maris, 2019 a hanyar Kakuki zuwa Kankara, jihar Katsina. Kakakin 17 Brigade, Laftanan Omoniyi, ya saki jawabi da ranan Talata, 27 ga watan Maris kan yadda suka cetosu.

Yace: "Za ku tuna cewa an yi garkuwa da Sheik Ahmed Suleiman, babban malamin addini da wasu mutane biyar na kungiyar Jammaatul Izalatul Bidia Wa Iqamatus Sunna. Wannan abin takaici ya faru ne a hanyar Kakumi zuwa Kankara dake karamar hukumar Kankara dake jihar Katsina ranar 14 ga wata Maris, 2019.

"A lokacin, babban hafsan sojin Najeriya, ya baiwa rundunar 17 Birged umurnin cetosu tare da wasu jami'an tsaro. Sashen leken asirin hukumar ta kaddamar da shirye-shiryen yadda za'a bankadosu.."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel