Wani Sanatan APC a kudancin Najeriya zai fito neman kujerar majalisar dattawa

Wani Sanatan APC a kudancin Najeriya zai fito neman kujerar majalisar dattawa

- Wani Sanatan APC da ke kudancin Najeriya ya ce sai inda karfin shi ya kare wurin neman kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa

- Yace muddin aka ba wa dan arewa kujerar to jam'iyyar APC bata yi adalci ba ko kadan

Tsohon gwamnan jihar Abia, Dr Orji Uzo Kalu ya nuna bukatarshi ta neman kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa, wanda za ayi nan ba da dadewa ba.

Ya kuma nemi jam'iyyar APC mai mulki da ta ba da kujerar ga dan yankin kudu maso gabas, don hakan shine adalci kuma hakan zai kawo zaman lafiya a kasa.

Rahotanni sun nuna cewar Sanatan ya yi bayanin ne a yau Larabar nan filin tashi da saukan jiragen sama na jihar Lagos.

Wani Sanatan APC a kudancin Najeriya zai fito neman kujerar majalisar dattawa
Wani Sanatan APC a kudancin Najeriya zai fito neman kujerar majalisar dattawa
Asali: Facebook

Ya ce ya fuskanci cewa jam'iyyar APC wacce ita ce ta ke da mafi rinjaye na Sanatoci, amma ta dauki duka manyan kujerun majalisar dattawan ta kai su yankin arewa maso gabas, da kuma arewa maso yamma.

A cewar shi, a tsarin dokar kasa, ya ba wa 'yan majalisa damar da za su zabi shugabannin da za su jagorancesu a majalisa. Hatta shugaban kasa Muhammadu Buhari, da kuma shugaban jam'iyyar APC na kasa Mr. Adams Oshiomhole sun san da wannan dokar.

"Saboda haka in dai har adalci za ayi to dole ne a ba wa dan yankin kudu maso gabas kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa.

KU KARANTA: Gobara ta kone gidaje sama da 150 a jihar Jigawa

"Shugaban jam'iyya ya fito daga yankin kudu maso kudu, shugaban kasa ya fito daga yankin arewa maso yamma, mataimakin shugaban kasa ya fito daga kudu maso yamma, ga kuma shugaban majalisar dattawa zai fito daga arewa maso gabas.

"A gani na yarukan Najeriya, Ibo ne Yoruba, da kuma Hausa, saboda haka zanyi iya bakin kokari na wurin ganin na karbo kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawan nan.

"Hakan ba ya na nuna cewa ina fada da jam'iyya ba ne a'a sai dai hakan yana nufin nema wa kai adalci. Buhari da kanshi ya ce bayan zabe zai fara magana akan rashin adalci, kuma wannan matsalar ita ma tana daya daga cikin rashin adalcin," in ji Kalu.

Ya kara cewa sai iya inda karfinshi ya kare muddin ba a ba su kujerar mataimakin shugabana majalisar dattawa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel