Akwai yiwuwar a sake sabon zaben shugaban kasa a Najeriya

Akwai yiwuwar a sake sabon zaben shugaban kasa a Najeriya

- Shugaba Buhari dai na ta kara fuskantar barazana a kujerar shi inda jam'iyyu da dama suke zuwa Kotu da bukatar a sake sabon zabe

- Haka shima dan takarar shugaban kasa na babbar jam'iyyar adawa ta PDP wato Alhaji Atiku Abubakar shine ya fara tunkarar kotun da nufin cewa shi fa bai yadda da zaben da aka gudanar ba

A yanzu haka dai shugaban kasa Muhammadu Buhari na kara fuskantar wasu kalubale, yayinda wasu masu neman kujerar shugaban guda uku suka nufi Kotun daukaka kara dake Abuja, akan su ma ba su yadda da sakamakon zaben da aka gudanar ba a ranar 23 ga watan Fabrairun da ya gabata.

Akwai yiwuwar a sake zaben shugaban kasa a Najeriya
Akwai yiwuwar a sake zaben shugaban kasa a Najeriya
Asali: Facebook

Karar da 'yan takarar suka kai sun nemi kotu ta soke sakamakon zaben da aka gudanar, wanda shine ya ba wa shugaba Buhari damar zama shugaban kasa a karo na biyu.

Mutane ukun da suka kai karar sun hada da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Hope Democratic Party (HDP), Cif Ambrose Owuru, wanda ya samu kuri'u 1,663 a zaben da aka yi.

KU KARANTA: Gobara ta kone gidaje sama da 150 a jihar Jigawa

Sai kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Peoples Democratic Movement (PDM), Pastor Aminchi Habu. Sannan sai dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Coalition for Change (C4C), Geff Chizee Ojinka, wanda ya samu kuri'u 2,391

A karshe masu karar sun bukaci kotu ta soke zaben da aka gabatar ranar 23 ga watan Fabrairun da ya gabata, sannan a sake gabatar da wani sabon zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel