Rundunar yan sanda ta tabbatar da sakin Sheikh Ahmad Suleiman da wasu a Katsina

Rundunar yan sanda ta tabbatar da sakin Sheikh Ahmad Suleiman da wasu a Katsina

Rundunar yan sanda a jihar Katsina ta tabbatar das akin shahararren malamin nan mazaunin Kano, Sheikh Ahmad Suleiman da wasu mutane biyar, da aka sace a jihar Katsina kwanaki 12 da suka gabata.

Kakakin yan sandan jiharm Gambo Isa, ne ya tabbatar da lamarin ga kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a ranar Laraba, 27 ga watan Maris.

Ya bayyana cewa an saki Suleiman, wanda ya kasance shahararren makarancin Al-Qur’ani, da sauran wadanda aka sace da misalin karfe 4 na tsakar daren ranar Laraba.

Isa ya bayyana cewa wadanda abun ya shafa sun zanta da yan’uwansu sannan daga bisani yan sanda suka kwashe su sannan suka sada su da iyalansu.

KU KARANTA KUMA: Galadima yace lallai akwai ha’inci a sakamakon zaben Shugaban kasa

Kakakin yan sanda ya bayyana cewa ba a biya kudin fansa ba ga masu garkuwan kafin su sake su.

Idan za a tuna, a kwanaki 12 da suka gaabata ne aka sace malamain tare da wasu mutane a hanyar Sheme zuwa Kankara, a hanyarsu ta dawwa daga jihar Kano, bayan halartan wani taro na addini a jihar Kebbi.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Hukumar sojin Najeriya ta bayyana yadda ta ceto babban malamin addini, Sheik Ahmad Suleiman, da mukarrabansa guda biyar da akayi garkuwa da su ranar 14 ga watan Maris, 2019 a hanyar Kakuki zuwa Kankara, jihar Katsina.

Kakakin 17 Brigade, Laftanan Omoniyi, ya saki jawabi da ranan Talata, 27 ga watan Maris kan yadda suka ceto su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel