Galadima yace lallai akwai ha’inci a sakamakon zaben Shugaban kasa

Galadima yace lallai akwai ha’inci a sakamakon zaben Shugaban kasa

Kakakin kungiyar kamfen din takarar shugabancin Atiku Abubakar, Buba Galadima, ya dage cewa lallai sakamakon zaben shugaban kasa da ya bayyana shugaba Muhammadu Buhari a matsayin mai nasara karya ce kuma cike take da damfara.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 26 ga watan Maris a lokacin da ya bayyana a shirin Channels TV mai taken ‘Politics Today’, inda ya bayyana ra’ayinsa game da ikirarin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), cewa yawan kuri’unsu ya fi na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Mista Galadima dai har ila yau, bai bayyana asalin inda labarin ya fito ba ko da yake jam’iyyar ta gabatar da rubutacciyar kara a baya, inda tayi ikirarin cewa kuri’unsu yafi na Jam’iyyar APC da tazaran milyan 1.6.

Galadima duk da haka, ya karfafa cewa martanin jam’iyyar ya nuna cewar sun tsorata, saboda a cewar shi basu yi nasara ba.

Galadima yace lallai akwai ha’inci a sakamakon zaben Shugaban kasa
Galadima yace lallai akwai ha’inci a sakamakon zaben Shugaban kasa
Asali: UGC

Wani lauya, Uche Onu, wanda ya kasance bako a shirin har ila yau, ya mayar da martani ga cecekucen cewar karar da APC ta rubuta zai zamo a matsayin barazana ga jam’iyyar adawa.

KU KARANTA KUMA: Hukumar INEC ta bai wa zababben gwamna da yan majalisan jihar Borno takardun shaidan cin zabe

A cewar shi, jam’iyyar adawa na da yancin zuwa kotu don gabatar da rashin amincewar ta.

Don haka ya bayyana cewa, laifi newani mutum ya shiga na’urar kwamfuta ya kwashi wasu bayanai ba bias doka ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel