Yadda muka ceto Alaramma Ahmed Suleiman da mukarrabansa - Hukumar Soji (Hotuna)

Yadda muka ceto Alaramma Ahmed Suleiman da mukarrabansa - Hukumar Soji (Hotuna)

Hukumar sojin Najeriya ta bayyana yadda ta ceto babban malamin addini, Sheik Ahmad Suleiman, da mukarrabansa guda biyar da akayi garkuwa da su ranar 14 ga watan Maris, 2019 a hanyar Kakuki zuwa Kankara, jihar Katsina.

Kakakin 17 Brigade, Laftanan Omoniyi, ya saki jawabi da ranan Talata, 27 ga watan Maris kan yadda suka cetosu. Yace:

"Za ku tuna cewa an yi garkuwa da Sheik Ahmed Suleiman, babban malamin addini da wasu mutane biyar na kungiyar Jammaatul Izalatul Bidia Wa Iqamatus Sunna. Wannan abin takaici ya faru ne a hanyar Kakumi zuwa Kankara dake karamar hukumar Kankara dake jihar Katsina ranar 14 ga wata Maris, 2019.

A lokacin, babban hafsan sojin Najeriya, ya baiwa rundunar 17 Birged umurnin cetosu tare da wasu jami'an tsaro. Sashen leken asirin hukumar ta kaddamar da shirye-shiryen yadda za'a bankadosu.."

Yadda muka ceto Alaramma Ahmed Suleiman da mukarrabansa - Hukumar Soji (Hotuna)
Hukumar Soji (Hotuna)
Asali: Facebook

Wannan yunkuri ya kai ga ceto wadanda akayi garkuwa da su mislain karfe daya na daren yau. Malaman da aka ceto na cikin koshin lafiya kuma an asibitin rundunar ta duba su."

"Jim kadan bayan hira da manema labarai, an yi shirye-shiryen kaisu wajen mai martana sarkin Katsina, domin mikasu ga iyalansu."

Yadda muka ceto Alaramma Ahmed Suleiman da mukarrabansa - Hukumar Soji (Hotuna)
Yadda muka ceto Alaramma Ahmed Suleiman da mukarrabansa - Hukumar Soji (Hotuna)
Asali: Facebook

Yadda muka ceto Alaramma Ahmed Suleiman da mukarrabansa - Hukumar Soji (Hotuna)
Yadda muka ceto Alaramma Ahmed Suleiman da mukarrabansa - Hukumar Soji (Hotuna)
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel