Fasto ya bawa makarantar Islamiyya gudunmuwar allunan karatu a Kaduna

Fasto ya bawa makarantar Islamiyya gudunmuwar allunan karatu a Kaduna

Wata tawagar malaman addinin Kirista karkashin jagorancin Fasto Yohanna Buru ta rabawa makarantun Islamiyya allunan karatun Al-Kur'ani mai girma guda 100 da wasu kayayakin karatu a jihar Kaduna.

Prime Time News ta ruwaito cewa an bayar da gudunmuwar kayan karatun ne a wasu makarantun Islamiya a Rigasa, Bakin Ruwa, Mando da wasu sassan karamar hukumar Igabi.

A jawabin da ya yi a wurin bikin bayar da tallafin, Mr Buru ya ce sun bayar da gudunmawar ne saboda karfafa dankon zumunci da zaman lafiya tsakanin musulmi da kirista a jihar.

A cewarsa, kayayakin karatun da aka rabar za su taimakawa dalibai wurin koyon ilimi addinin musulunci da harshen larabci.

Fasto ya bawa makarantar Islamiyya gudunmuwar allunan karatu a Kaduna
Fasto ya bawa makarantar Islamiyya gudunmuwar allunan karatu a Kaduna
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dattaku: Ganduje ya bayar da umurnin a mayar da hotunan Sarki Sanusi II a gidan gwamnati

Ya yi kira ga musulmi da kirista a Najeriya su cigaba da kokarin ganin an samu zaman lafiya, hadin kai da cigaba a Najeriya.

"Mun rabar da allunan karatun sama da 100 da wasu kayayakin karatu domin tallafawa ilimin almajirai a Kaduna," inji Buru.

Faston ya yi kira fa shugabanin addini da al'umma a jihar su cigaba da kiran mabiyansu su zauna lafiya.

"Coci ba za ta taba manta abin alherin da wata musulma, Hajiya Ramatu Tijjani tayi ba na bayar da gudunmawar Bible guda 50.

"Har ila yau matar da rabawa zaurawa da marayu zannuwa da kayan abinci domin suyi shagalin Kirsimeti da sabon shekara," inji shi.

Ya kuma yi kira ga UNESCO, UNICEF da gwamnatin bayar da gudunmawa domin inganta karatun makarantun allo.

A yayin da ya ke karbar gudunmawar, wani malami a Rigasa, Lawal Maduru (Galadiman Tudun Wada) ya yabawa hangen nesan faston inda ya ce tallafin zai taimaka wurin hada kan al'ummar musulmi da kirista a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel