An yiwa yara 80,468 rigakafin shan inna a Daura

An yiwa yara 80,468 rigakafin shan inna a Daura

- Cutar shan inna ya fara zama tarihi a arewacin Najeriya

- Gwamnatocin jiha basuyi kasa a gwiwa wajen kawo karshen wannan cuta ba

- A garin Daura mahaifar shugaban kasa, yara dubu tamanin da yan kai sun samu rigakafin

An yiwa kananan yara 80,468 rigakafin shan inna a karamar hukumar Daura dake jihar Katsina a atisayen rigakafin da aka kammala a watan Maris, 2019.

Diraktan kiwon lafiyan yara da mata, Malam Murtala Ahmed, ya bayyana hakan ne ranar Talata, 27 ga watan Maris, 2019.

Ya ce ma'aikatar ta samu magungunan rigakafi 87,020 kuma ta bayar da 86,900 a fadin unguwanni 11 dake yankin, inda aka samu nasarar baiwa kusan dukkan yaran da ke karamar hukumar.

KU KARANTA: Kotu ta yanke wa makashin yar tsohon mataimakin gwamnan Ondo hukuncin kisa

Ya kara da cewa gidaje 34 masu yara 59 kadai ne basu samu wannan rigakafi ba. Amma ya bada tabbacin cewa za'a basu rigakafin muddin aka fara zagaye na biyu ba da dadewa ba.

"Zamu tabbatar da cewa babu yaron da aka bari a baya."

Dirakta Murtala ya yabawa al'ummar karamar hukumar, musamman iyaye bisa ga goyon bayan da suka bada wajen baiwa yaransu rigakafin.

NAN ta bada rahoton cewa a shekarar 2018, an baiwa yara a karamar hukumar Daura 80,367 irin wannan rigakafi.

Kana a makon da ya gabata, ma'aikatar ta kaddamar da shirin wayar da kan jama'a kan ciwon sankarau, da kuraje saboda canjin yanayi da aka samu a fadin kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel