Da duminsa: Ihedioha da 'yan majalisu 27 sun karbi takardar shaidar cin zabe a Imo

Da duminsa: Ihedioha da 'yan majalisu 27 sun karbi takardar shaidar cin zabe a Imo

- INEC a ranar Laraba ta rabawa zababben gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha takardar shaidar cin zabe

- Hukumar zaben ta kuma gabatar da takardar cin zaben ga 'yan majalisu 27 da aka zaba zuwa majalisar dokokin jihar

- Ihedioha ya sha alwashin nuna adalci a dukkanin bangaren shugabancinsa ba tare da duba banbanci ko da na siyasa ba

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a ranar Laraba ta rabawa zababben gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha takardar shaidar cin zabe.

Kwamishinan hukumar na jihar, Farfesa Francis Ezeonu, wanda ya jagoranci bukin rabon takardun, ya kuma gabatar da takardar cin zaben ga 'yan majalisu 27 da aka zaba zuwa majalisar dokokin jihar.

Ihedioha ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris karkashin jam'iyyar PDP.

KARANTA WANNAN: Rundunar soji ta sha alwashin hukunta wadanda suka kashe sojoji a Abonnema

Da duminsa: Ihedioha da 'yan majalisu 27 sun karbi takardar shaidar cin zabe a Imo
Da duminsa: Ihedioha da 'yan majalisu 27 sun karbi takardar shaidar cin zabe a Imo
Asali: UGC

Da ya ke jawabi jim kadan bayan karbar takardar shaidar cin zaben a ofishin hukumar INEC da ke Oweri, babban birnin jihar, Ihedioha ya sha alwashin nuna adalci a dukkanin bangaren shugabancinsa ba tare da duba banbanci ko da na siyasa ba.

Ya ce zai bi dokokin da suka wajaba a a kansa yayin gudanar da mulkin jihar.

Ya ba da tabbacin cewa mukarraban gwamnatinsa za su kasance maza da mata da ke da kima wadanda kuma za su bada gudunmowarsu wajen bunkasa jihar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel