Jam’iyyar APC na shirin kaurace ma zaben Adamawa da za a sake a ranar Alhamis

Jam’iyyar APC na shirin kaurace ma zaben Adamawa da za a sake a ranar Alhamis

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Adamawa, ta yi barazanar kaurace ma zaben gwamna da za’a sake idan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta dage cewan zata gudanar da zaben a ranar Alhamis, 2 ga watan Maris.

Sakataren tsare-tsare na jam’iyyar APC, Alhaji Ahmed Lawan, ya bayyana matsayar jam’iyyar a ranar Laraba, 26 ga watan Maris a Yola.

Lawan ya fada wa kamfanin Dillancin Labarai (NAN) cewa jam’iyyar ta nuna rashin amincewa da zabe a ranar Alhamis kuma ta sanar da hukumar zaben matsayin ta.

Jam’iyyar APC na shirin kaurace ma zaben Adamawa da za a sake a ranar Alhamis
Jam’iyyar APC na shirin kaurace ma zaben Adamawa da za a sake a ranar Alhamis
Asali: Depositphotos

NAN ta rahoto cewa INEC ta bayyana Alhamis a matsayin ranar sake zabe a wuraren zabe 44.

Wannan ya biyo bayan dage hukuncin baya da kotun tayi na hana gudanar da zaben a ranar Asabar da ya gabata.

KU KARANTA KUMA: Kudi ba zai taba chanja ra’ayin mutane ba – PDP Sokoto ta nemi APC ta yarda da shan kaye

A nashi bangaren Shugaban jam’iyyar PDP a Adamawa, Mista Tahir Shehu, wanda dan takararsu Ahmadu Fintiri ke kan gaba da tazaran kuri’u 30,000, ya ce a shirye suke don gudanar da zaben.

A lokacin da aka tuntubi kwamishinan hukumar zabe (INEC) a Adamawa, Mista Kassim Gaidam, ya bayyana cewa hukumar zata gudanar da zaben kamar yanda ta shirya a ranar Alhamis.

Gaidam ya bukaci dukkan jam’iyyun dasu yi aiki don tabbatar da zabe ba tare da kalubale ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel