Kudi ba zai taba chanja ra’ayin mutane ba – PDP Sokoto ta nemi APC ta yarda da shan kaye

Kudi ba zai taba chanja ra’ayin mutane ba – PDP Sokoto ta nemi APC ta yarda da shan kaye

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen Jihar Sokoto, ta bukaci jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ta amince da shan kayi a zaben gwamna sannan ta daina zarge-zargen karya.

A wani jawabi da ta fitar a ranar Talata, jam’iyyar tayi wa APC a jihar ba’a akan kaye da ta sha a zabe “duk da hayan yan bangan siyasa da siyan kuri’u da tayi”.

Dan takaran PDP Aminu Tambuwal ya doke Ahmed Aliyu na jam’iyyar APC a zaben gwamna da tazarar kuri’u 342, wanda ya kasance tazara mafi karanci a tarihin zaben Najeriya.

Amman jam’iyyar APC ta ki amincewa da nasarar, yayin da tayi zargin murdiya da rashin gudanar da zaben cikin lumana.

Kudi ba zai taba chanja ra’ayin mutane ba – PDP Sokoto ta nemi APC ta yarda da shan kaye
Kudi ba zai taba chanja ra’ayin mutane ba – PDP Sokoto ta nemi APC ta yarda da shan kaye
Asali: Twitter

A jawabin da kakakin jam’iyyar PDP a jihar, Abdullahi Yusuf ya gabatar a Sokoto, jam’iyyar tayi watsi da ikirarin jam’iyyar APC, yayin da ta zarge su da yunkurin murde zaben.

“Saboda haka, abunda yafi dacewa ga jam’iyyar adaawa ita ce kawai amincewa da shan kayi, sannan ta nemi hanyar sasantawa da masu basu gudumuwa na kudi, cewa babu adadin kudi da zai sa mutanen Sokoto masu kirki su canja biyayyar su ba ga Mutawalle, gwamnatinsa da yan uwansa na siyasa.

KU KARANTA KUMA: Kwanakin mulkin ka kirgaggu ne – Wata kungiya ga Tambuwal

“A matsayinku na masu kishin kasa kuma masu biyayya da zaben gaskiya , kuma masu yarda da adalci, jam’iyyar APC mai adawa ta lura da abunda ya faru da Napoleon Hill, cewa “idan ka sha kayi, ka amince da hakan a matsayin gargadin cewa shirye shiryenka basu hadu ba, sai ka sake yin sabon shirin, sannan kayi kokarin cimma burin ka.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel