Yanzu Yanzu: Kotu ta yanke wa makashin yar tsohon mataimakin gwamnan Ondo hukuncin kisa

Yanzu Yanzu: Kotu ta yanke wa makashin yar tsohon mataimakin gwamnan Ondo hukuncin kisa

Wata babbar kotun jihar Ondo da ke zama a Akure, ta yanke wa Seidu Adeyemi hukuncin kisa ta hanyar rataya, a kan laifin Khadijat Oluboyo, diyar tsohon mataimakin gwamnan jihar Ondo.

An gurfanar da Adeyemi ne bisa laifin kashe budurwarsa, Khadijat a ranar 2 ga watan Yuli, 2018 sannan ya binne ta cikin dakinsa a Aratusi, a yankin Oke-Aro dake Akure.

Khadijat ta kasance dalibar mataki na karshe a jami’ar Ajasin dake Akungba Akoko (AAUA) kafin mutuwar ta.

Yanzu Yanzu: Kotu ta yanke wa makashin yar tsohon mataimakin gwamnan Ondo hukuncin kisa
Yanzu Yanzu: Kotu ta yanke wa makashin yar tsohon mataimakin gwamnan Ondo hukuncin kisa
Asali: Twitter

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, hukumar Yan sandan Najeriya reshen jihar Ondo ta gurfanar da Alao Adeyemi a gaban kotun Majistare dake Akure, babban birnin jihar Ondo.

Adeyemi tare da wasu mutane biyu ne suka hada baki suka yiwa Khadijat kisar gilla a dakin Adeyemi kuma suka birne gawarta a karkashin gadonsa a gidansa dake unguwar Aratusin dake Akure kafin daga baya aka kama shi.

KU KARANTA KUMA: Kwanakin mulkin ka kirgaggu ne – Wata kungiya ga Tambuwal

A yayin gudanar da shari'ar, Dan sanda mai shigar da kara, Saja Mary Adebayo ta bukaci kotu ta tsare wanda ake tuhumar a kurkuku gabanin lokacin da za'a samu shawarar lauyoyi daga sashin hulda da jama'a DPP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel