Yanzu Yanzu: Atiku da PDP sun samu yardar kotu na mika takarda ga Buhari ta hannun APC

Yanzu Yanzu: Atiku da PDP sun samu yardar kotu na mika takarda ga Buhari ta hannun APC

Kotun zabe na Shugaban kasa ta amince da bukatar jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) da dan takararta a zaben Shugaban kasa da aka yi, Atiku Abubakar na neman izinin mika takardar kararsu ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta hannun jam’iyyarsa, All Progressives Congress (APC).

PDP da Atiku, wadanda suka shigar da kara a farkon watan nan inda suke kalubalantar nasarar Buhari a zaben shugaban kasa, sun bayar da uzurin cewa suna fuskantar matsala wajen bashi takardar kai tsaye.

A ranar Laraba, 27 ga watan Maris kotun zaben wanda ke dauke da mutane uku, bayan sauraron korafin da suka gabayar Chris Uche (SAN) ya basu izinin mika takardar karan ta wani siga daban.

Yanzu Yanzu: Atiku da PDP sun samu yardar kotu na mika takarda ga Buhari ta hannun APC
Yanzu Yanzu: Atiku da PDP sun samu yardar kotu na mika takarda ga Buhari ta hannun APC
Asali: Twitter

Justis Abdul Aboki, wanda ja jagoranci zaman, ya yi umurnin cewa ana iya mika wa Buhari takardar ta hannun kowani babban jami'i na APC a sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja.

KU KARANTA KUMA: Ku tuna da Kirista wajen rabon mukaman majalisar tarayya - Kungiya ta bukaci APC

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, a ranar Laraba, kotun daukaka da ke zaman ta a garin Abuja za ta fara sauraron korafi na kalubalantar sakamakon zabe da dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gabatar ma ta.

Atiku Abubakar, da ya kasance tsohon mataimaikin shugaban kasar Najeriya, na ci gaba da rashin amincewa tare da kalubalantar sakamakon zaben kujerar shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun 2019.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel