Kwanakin mulkin ka kirgaggu ne – Wata kungiya ga Tambuwal

Kwanakin mulkin ka kirgaggu ne – Wata kungiya ga Tambuwal

Biyo bayan sharhin da ake tayi akan zaben gwamna da aka kammala kwanan nan a jihar Sokoto, wata kungiya ta gargadi Aminu Tambuwal zababben gwamnan jihar da kada yayi murnar nasararsa tukuna.

Haka zalika kungiyar mai suna ‘Agenda for Democracy and Good Governance’ ta bukaci Tambuwal da ya kyale rundunar sojin Najeriya yayinda yake dandana nasara mara dorewa, wanda ba tsere ma doka ba.

Shugaban kungiyar na kasa, Gambo Muhammadu, yace yunkurin Tambuwal na ganin laifin rundunar soji kan faduwar da yayi a zahiri wani yunkuri ne na son kare kanshi daga fattakar da kutun zabe za ta yi masa.

Kwanakin mulkin ka kirgaggu ne – Wata kungiya ga Tambuwal
Kwanakin mulkin ka kirgaggu ne – Wata kungiya ga Tambuwal
Asali: Twitter

Muhammadu a wata sanarwa yace kungiyar ta lura da yunkurin zababben gwamnan na son amfani da kokarin sojoji na hana satar akwati a matysayin makamin wofantar da kuri’un da jama’a suka yi a jihar.

KU KARANTA KUMA: Mu da muka yi wahala ne ya kamata mu jagoranci majalisa - Gudaji Kazaure

Yace kungiyar ta ga cewa akwai bukatar daidaita Tambuwal saboda irin wannan yunkuri da gwamnan na jihar Sokoto ke yi na son daura laifi akan sauran masu ruwa da tsaki a jihar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal a jiya, Litinin, 25 ga watan Maris ya ba wa mutanen jihar tabbacin cewa, babu mai juya shi a mulkinsa na biyu.

Ya bayyana cewa ba zai taba manta nasarar da yayi da kuri’u 342 ba. “Aikin Allah ne idan aka duba abunda ya faru a lokacin zabe,” cewar shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel