Shugabancin majalisar dattijai: APC ta sha alwashin ladabtar da Ndume kan bijire mata

Shugabancin majalisar dattijai: APC ta sha alwashin ladabtar da Ndume kan bijire mata

- Rahotanni na nuni da cewa tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai, Sanata Ali Ndume na iya shiga cikin matsala da jam'iyyar APC

- Ndume dai ya bijirewa matsayar jam'iyyar APC na tsayar da Sanata Ahmad Lawan a matsayin shugaban majalisar dattijai

- A bangaren APC, ta ce za ta dauki matakan ladabtarwa akan duk wani mambanta da ya bijire mata ko ya ke adawa da wani mataki da ta dauka

Jam'iyyar APC ta ce za ta dauki matakan ladabtarwa ga duk wani mambanta da ta same shi da yin adawa ko bijirewa duk wani matakin da ta dauka akan shugabancin majalisar tarayyar kasar ta tara.

Sakataren watsa labarai na jam'iyyar na kasa, Malam Lanre Issa-Onilu ya bayyana wannan matsayar ta jam'iyyar, bayan da tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai Sanata Ali Ndume ya bijirewa matsayar APC na tsayar da Sanata Ahmad Lawan a matsayin shugaban majalisar dattijhjai.

Ndume (APC, Borno ta Kudu) ya shaidawa manema labarai a Abuja cewar matsayar jam'iyyar kamar yadda shugabanta na kasa Adams Oshiomhole a ranar 25 ga watan Maris ya tsayar da Lawan a matsayin shugaban majalisar dattijai da Hon. Femi Gbajabiamila a matsayin kakakin majalisar wakilan tarayya tamkar cin fuskane kuma ya sabawa dokar kasar.

KARANTA WANNAN: Sakamakon damfarar N5.6m: Wani malamin tsubbu zai shafe shekaru 97 a kurkuku

Shugabancin majalisar dattijai: APC ta sha alwashin ladabtar da Ndume kan bijire mata
Shugabancin majalisar dattijai: APC ta sha alwashin ladabtar da Ndume kan bijire mata
Asali: Facebook

Da ya ke zantawa da jaridar ThisDay akan wannan jawabi na Ndume, Issa-Onilu ya ce duk wani yunkuri da wani mamban jam'iyyar zai yi na bijirewa matsayar jam'iyyar zai tilasta jam'iyyar ta dau matakin ladabtarwa.

Ya ce jam'iyyar ba ta tsammani wani daga cikin mambobinta zai kalubalanci matsayar da ta dauka na raba shugabancin majalisar tarayyar ta tara akan tsarin shiyya shiyya.

Ya ce: "Idan har ka kalubalanci matsayar jam'iyya, hakan na nufin rashin ladabi kuma dokokinmu na nan na ladabtarwa akan masu bijirewa jam'iyya."

Da ya ke karin haske kan yadda jam'iyyar ta zabi Lawan a matsayin shugaban majalisar dattijai, Onilu ya ce sai da jam'iyyar ta fara tuntubar manyan shuwagabanni da masu ruwa da tsaki, daga bisani kuma jam'iyyar ta kai maganar gaban shugaban kasa domin neman shawarwarinsa.

A ranar 25 ga watan Maris ne Ndume ya aikewa shuwagabannin APC da takarda, inda ya ke bayyana masu ra'ayinsa na tsayawa takarar kujerar majalisar dattijai ta 9 bayan an kafa ta a cikin watan Yuni.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel