Wani ma'aikacin kotu ya rasa ransa saboda gwamnati ta hana shi albashi

Wani ma'aikacin kotu ya rasa ransa saboda gwamnati ta hana shi albashi

- Gwamnoni da yawa basa iya biyan albashin ma'aikata, hakan ya yi sanadiyyar mutuwar wani ma'aikacin kotu, saboda gwamnatin jihar su ta shafe wata tara ba ta biya su albashi ba

- Ma'aikatan kotun sun roki mutane su taya su da addu'a Allah yasa gwamnati ta biya su, saboda suna cikin wani mawuyacin hali

Mutane sun sake shiga damuwa, bayan mutuwar Zekery Aguye, tsohon majistire, kuma mataimakin rijistara na babbar kotun jihar Kogi. Mutuwar ta shi da aka alakanta ta da rashin biyan albashi da alawus da gwamnatin jihar ta daina yi.

Aguye, wanda yake fama da ciwon daji, ya tilastawa kanshi daina zuwa asibiti, saboda ba shi da kudin sayen magani.

Yahaya Adamu, rijistara na babbar kotun jihar ta Kogi, ya alakanta mutuwar Aguye da rashin kudi, inda ya ce za a iya nema mishi magani da ace ba a daina biyansu albashi ba.

Wani ma'aikacin kotu ya rasa ransa saboda gwamnati ta hana shi albashi
Wani ma'aikacin kotu ya rasa ransa saboda gwamnati ta hana shi albashi
Asali: UGC

Ya ce: "Abun ya samo asali a lokacin da muke tunanin rashin lafiyar tashi ba mai tsanani ba ce, sai daga baya muka gane cewa yana bukatar ya ga kwararren likita, sai muka je asibitin tarayya, da taimakon 'yan uwanshi dana abokanan arziki, ya dan samu lafiya.

"Sai likitocin su ka bashi magunguna, inda kudin maganin ya kai kimanin N500,000, kowanne wata."

Adamu ya ce tilas ta sanya mamacin ya daina karbar magani saboda bashi da kudin da zai iya biyan kudin maganinshi, tun lokacin da aka daina biyansu albashi.

KU KARANTA: Kahutu Rarara: Dalilin da ya sa nayi wakar 'Ta leko ta labe'

Adamu ya roki gwamnan jihar ta Kogi Yahaya Bello, akan ya baiwa ma'aikatan shari'a hakkinsu, saboda kada a kara samun irin wannan matsalar nan gaba.

"Yanzu maganar nan da nake da ku, mutane da yawa suna asibiti, 'ya'yansu da yawa an kore su daga makaranta saboda basu biya kudin makaranta ba, wasu ma ba su da gidajen zama, saboda basu da kudin haya.

"Ina so na yi amfani da wannan damar na roki 'yan Najeriya su taya mu rokon mai girma gwamna Yahaya Bello, ya taimaka ya biya ma'aikatan shari'a albashinsu, saboda mu biya bashin da ake bin mu na wata tara."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel