Kungiyar Kiristocin Kaduna sun yi tir da yadda ake satar Bayin Allah

Kungiyar Kiristocin Kaduna sun yi tir da yadda ake satar Bayin Allah

Jaridar Daily Trust ta kasar nan ta rahoto cewa Kungiyar CAN ta Mabiya addinin Kirista na reshen jihar Kaduna sun koka game da yadda satar jama’a a Gari babu gaira babu dalili ya zama ruwan dare a yau.

Kungiyar ta CAN tace satar Bayin Allah da ake yi, ya nuna gazawar gwamnatin Najeriya wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar. Kungiyar tayi wannan magana ne ta bakin shugaban ta na Kaduna watau John Joseph Hayab.

Rabaren John Joseph Hayab, wanda shi ne ke jagorantar kungiyar ta Kirista a jihar Kaduna, yayi wannan jawabi ne bayan an sace wani babban Limamin addinin na Kirista, John Bako Shekwolo, na cocin Theresa Catholic da ke jihar.

KU KARANTA: Murna ta ko ina bayan Alaranman da aka sace ya kama hanyar dawowa gida

Kungiyar Kiristocin Kaduna sun yi tir da yadda ake satar Bayin Allah
CAN tayi Allah-wadai da yadda ake satar mutane babu kaukautawa
Asali: Facebook

John Bako Shekwolo da aka sace kwanan nan, shi ne babban Limamin Katolika na Ankwa da ke cikin karamar hukumar Kachia. John Hayab yace garkuwa da mutane ya zama hanyar samun kudi yanzu a Kaduna saboda sakacin hukuma.

Shugaban CAN din ya nemi ayi a maza a saki babban Malamin na Darikar Katolika watau Rabaren Bako Shekwolo ba tare da wani abu ya faru da shi ba. Shehin yace idan ba a fito an yi magana ba, ba za a kawo karshen yin garkuwa da mutane ba.

Babban Limamin ya kuma yi kira ga jama’a su fito su rika fadawa gwamnati gaskiyar abin da ke faruwa sannan yace jami’an tsaro su tashi tsayin-daka wajen ganin sun yi abin da ya dace na kare ran Bayin Allah da kuma tsare dukiyoyinsu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel