Rundunar soji ta sha alwashin hukunta wadanda suka kashe sojoji a Abonnema

Rundunar soji ta sha alwashin hukunta wadanda suka kashe sojoji a Abonnema

- Rundunar soji ta sha alwashin hukunta duk wadanda ta kama da hannunsu a kisan da aka yiwa jami'anta da sauran fararen hula a garin Abonnema

- Rundunar sojin ta kuma roki al'ummar garin Abonnema da su taimaka mata da muhimman bayanai da za su kaita ga cimma gaci kan lamarin

- A nashi bangaren, Sarkin Abonnema ya jaddada kyakkyawan yakininsu akan rundunar sojin tare da bukatar matasan garin da su nuna dattako

Rundunar soji ta sha alwashin hukunta duk wanda ta kama da sa hannu a kisan da aka yiwa jami'anta da sauran fararen hula a garin Abonnema a zaben da aka gudanar makonnin da suka gabata.

Rundunar sojin ta sanar da hakan a ranar Talata a Abonnema, karamar hukumaar Akuku-Toru da ke jihar Rivers a lokacin da wani kwamitin bin diddigi, karkashin jagorancin Manjo Janar Taritimiye Gagariga, ya kai ziyara ga Amanyanabo na garin, Sarki Disrael Bob-Manuel.

Gagariga ya bayyana cewa rundunar soji za ta kasance mai yin adalci a lokacin da ta zo yanke hukunci kan lamarin, yana mai cewa duk wanda aka kama da hannu a kashe kashen zai fuskantaci hukunci.

KARANTA WANNAN: Sabon rahoto: Facebook ya lalata shafuka 2,632 da suka karya dokokin kamfanin

Rundunar soji ta sha alwashin hukunta wadanda suka kashe sojoji a Abonnema
Rundunar soji ta sha alwashin hukunta wadanda suka kashe sojoji a Abonnema
Asali: UGC

Gagariga wanda ya ke jawabi ga sarkin da kuma matasan garin ya ce: "Karku damu, wadanda suka haddasa rikici a Abonnema za su shiga hannu kuma zamu tabbata shari'a ta yi aiki a kansu.

"Idan har kuna da wani bayani da zai taimaka mana wajen warware wannan matsalar, ku taimaka ku sanar da mu."

Da ya ke na shi jawabin, Amanyanabo na garin ya bukaci matasa da su nuna dattako, yana mai cewa "Na san cewa wannan lamarin abun bakin ciki ne. Amma mu ci gaba da dora kyakkyawan yakininmu akan rundunar soji kuma na san cewa duk wadanda ke da hannu a kashe kashen za su fuskanci hukunci."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel