Ku tuna da Kirista wajen rabon mukaman majalisar tarayya - Kungiya ta bukaci APC

Ku tuna da Kirista wajen rabon mukaman majalisar tarayya - Kungiya ta bukaci APC

- Wata kungiyar addini ta mika kokon bararta ga Shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kan raba mukaman majalisa

- Kungiyar ta bukaci shugabancin APC da ta duba matsayin yawan addini da ke Najeriya saannan su yi daidaito wajen rabon mukamai ga manyan addinan kasar, wato addinin Islama da na Kirista.

- Tace majalisun dokokin kasar ta kunshi mambobi Musulmai da Kirista, don haka a kamanta adalci

Biyo bayan zargin cewa ana shirin ba da mukaman Shugaban majalisar dattawa, da kakakin majalisar wakilai da kuma mataimakin majalisar dattawa zuwa ga yankin arewa maso gabas, kudu maso yamma da kuma Arewa maso yamma, wata kungiyar addini ta mika kokon bararta ga Shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), da ta duba matsayin yawan addini da ke Najeriya sannan su yi daidaito wajen rabon mukamai ga manyan addinan kasar, wato addinin Islama da na Kirista.

Kakakin kungiyan, Appostle Kehinde Collins, yace APC tayi hakan domin tabbatar da kwanciyar hankali da hadin kai a Najeriya.

Ku tuna da Kirista wajen rabon mukaman majalisar tarayya - Kungiya ta bukaci APC
Ku tuna da Kirista wajen rabon mukaman majalisar tarayya - Kungiya ta bukaci APC
Asali: UGC

Ya karfafa cewa Majalissun na kasa sun kasance da mambobi musulmai da kirista.

Yayin da yake jawabi ga mambobin kungiyar, a ranar Litinin, 26 ga watan Maris, Collins ya bukaci shugabancin jam’iyyar APC da ta yi la’akari da yanayin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Mu da muka yi wahala ne ya kamata mu jagoranci majalisa - Gudaji Kazaure

Collins ya bukaci shuwagabannin addinai da suyi kira ga yan siyasa, sannan su yi roko ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, don tabbatar da cewa an ba kungiyoyin kabilu da na addinai dama iri guda.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel